Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka, Mike Pence, ya janye takararsa ta neman tikitin jam’iyyar Republican a yunkurinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2024.
Pence ya janye ne bayan da yi ta taga-taga wajen tara kudaden yakin neman zabe da kuma yadda ba ya samun karbuwa a kuri’ar neman jin ra’ayin jama’a.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya sanar da hakan ne a ranar Asabar a Las Vegas a wani taron shekara-shekara da Yahudawa ‘yan Republican suka yi.
“Alamu sun nuna karara cewa yanzu ba lokacina ba ne.” Pence ya ce.
Pence shi ne fitaccen dan takara na farko da ya janye takararsa yayin da tsohon mai gidansa da ya zama abokin hamayyarsa Donald Trump ya mamaye fagen takarar.
Sai dai Pence bai fadi dan takarar da zai goya wa baya ba, amma dai ya ci gaba da caccakar Trump.
Dandalin Mu Tattauna