Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sandra Day O'Connor, Macen Farko Da Ta Zama Alkalin Kotun Koli Ta Farko, Ta Mutu Tana Da Shekaru 93


Sandra Day O'Connor
Sandra Day O'Connor

Sandra Day O'Connor, wacce ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko mai shari'a a Kotun Koli, ta mutu da safiyar Juma'a ta na da shekaru 93.

O'Connor, wacce ta yi ritaya a shekara ta 2006, ta mutu a jiharta ta Arizona sakamakon ciwon mantuwa na kwakwalwa da kuma cutur numfashi.

Babban mai shari'a John Roberts ya fada a cikin wata sanarwa cewa O'Connor "ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko a kasarmu da ta zama alkali."

O'Connor ta girma ne a kan Lazy B, wani wurin kiwon shanu mai fadin eka 160,000 a cikin babban yankin hamada da ke kan iyakar Arizona da New Mexico.

Bayan shekaru hudu tana aiki a ofishin babban lauyan jihar Arizona, an nada ta don cike gurbin kujerar Majalisar Dattawan jihar a shekarar 1969. Bayan da aka sake zaben ta, sai ta zama mace ta farko a kasar da ta zama shugabar masu rinjaye na Majalisar Dattawan jihar.

A cikin 1981, a yayin da Shugaba Ronald Reagan ke neman wanda zai taimake shi ya cika alkawarin yakin neman zabe na nada mace a Kotun Koli, ya samu shawarwari game da ita masu mahimmaci. Lamarin da ya yi sandiyar cika wannan alkawarin. Ta yi kama da mai ra'ayin mazan jiya a yayin zamanta na tabbatar da Majalisar Dattawa, inda ta nuna adawa da ra'ayin cewa 'yancin zubar da ciki ya cancanci karewa a tsarin mulki.

"Ra'ayina a fannin zubar da ciki shine ina adawa da hakan a matsayin batun hana haihuwa ko akasin haka," in ji ta.

Nadin O'Connor a matsayin mace alkali ta farko mai adalci ba kawai ya kafa tarihi ba ne, ya kuma zaburar da wasu jihohi su fara sanya mata a kotun koli.

O'Connor ta bar 'ya'ya uku da jikoki shida. Mijinta ya rasu a shekara ta 2009.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG