Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Jinkirta Sulhun Musanyar Fursinoni Tsakanin Isra'ila Da Hamas


Benjamin Netanyahu
Benjamin Netanyahu

A yau Alhamis, Qatar ta sanar cewa dakatar da fada tsakanin Isra'ila da Hamas da kuma sako mutanen da aka yi garkuwa da su da fursunoni na iya zuwa nan gaba kadan, bayan jinkirin aiwatar da yarjejeniya tsakaninsu wanda kuma hakan zai taimakawa agajin jin kai zuwa zirin Gaza.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Qatar Majed Al-Ansari ya ce "Za a kammala yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma a cikin sa'o'i masu zuwa."

Majed Al Ansari.
Majed Al Ansari.

Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na Isra'ila, Tzachi Hanegbi, ya fada a cikin wata sanarwa da yammacin jiya Laraba cewa, ana ci gaba da tattaunawa, kuma ba za a sako mutanen farko da Hamas ta yi garkuwa da su a Gaza ba, sai akalla ranar Juma'a.

A karkashin yarjejeniyar dai Isra'ila za ta dakatar da kai hare-hare a zirin Gaza na tsawon kwanaki hudu. Hamas dai za ta saki mata da yara 50 da ta kama a harin da aka kai wa Isra’ila a watan Oktoba, kuma ana sa ran Isra’ila za ta sako fursunonin Falasdinawa 150.

Ba a bayyana ko daya daga cikin wadanda aka sako ba, sai dai jami'an Amurka sun ce suna sa ran cewa wasu daga cikin Amurkawa tara da ake kyautata zaton Hamas na rike da su na cikin wadanda aka sako.

Sojojin Isra'ila sun ce a ranar Alhamis din da ta gabata sun kai hare-hare ta sama kan wurare 300 na Hamas a ranar da ta gabata, wadanda suka hada da ramuka, dakunan ajiya da wuraren dakon tankokin yaki da mayakan ke amfani da su.

Sojojin Isra'ila
Sojojin Isra'ila

Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin tabbatar da cewa Hamas ba za ta sake iya kaiwa Isra'ila hari a nan gaba ba. Ya fada a wani taron manema labarai da yammacin Laraba cewa, bayan kawo karshen wa’adin tsagaita bude wuta, sojojin Isra’ila za su ci gaba da yakinsu a Gaza.

"Ina so in bayyana a fili, wannan yakin zai cigaba, wannan yakin zai cigaba za mu ci gaba da shi har sai mun cimma dukkan burinmu," in ji Netanyahu.

Isra'ila ta fara yakin soji na kawar da kungiyar Hamas bayan da kungiyar da Amurka ta ayyana a matsayin 'yan ta'adda ta kai hari a ranar 7 ga watan Oktoba. Isra'ila ta ce an kashe mutane 1,200 a wannan rana sannan kuma an yi garkuwa da kusan 240 zuwa Gaza.

Ma'aikatar lafiya ta Gaza a karkashin kungiyar Hamas ta ce Falasdinawa sama da 12,000 da suka hada da akalla yara 5,000 ne aka kashe a harin da sojojin Isra'ila suka kai a zirin Gaza.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG