Nan da zuwa karshen makon nan ne ake sa ran jam’iyyar Republican za ta tsayar da Donald Trump a matsayin dan takararta a hukumance, lamarin da zai baiwa masu kada kuri’a a Amurka damar yin zaben shugaban kasa a ranar 8 ga watan Nuwamba.
A yayin da ake shirye-shiryen zaben fidda ‘yan takarar shugabancin Amurka, sai gashi wasu sabbin zaben jin ra’ayi da aka gudanar a jiya Lahadi na nuna cewa Hillary Clinton ‘yar jam’iyyar
Mutumin da ake ganin shi jam’iyar Republican za ta tsayar dan takarar shugaban kasa a Amurka, Donald Trump, ya zabi gwamnan Indiana, Mike Pence a matsayin abokin takararsa.
Tsohuwar sakatariyar ma’aikatar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta shiga tarihi, a matsayin macen farko da za a tsayar takarar shugaban kasa karkashin manyan jam’iyun siyasar kasar biyu.
Wani sabon binciken jin ra’ayin Amurkawa da aka fitar da sakamakons a yau Litinin, ya nuna cewa, Amurkawa sun fi duba yiwuwar jefawa dan takarar Democrat, Bernie Sanders kuri’a, fiye da kowane dantakara da ya rage a yakin neman zaben 2016.
Ana ta ci gaba da gudanar da zaben fidda gwanayen da zasu tsaya takarar Shugabancin Amurka a karkashin jam’iyyar masu ra’ayin ‘yan mazan jiya ta Republican da kuma ta Democrat masu sassaucin ra’ayi.
Hillary Clinton na jam’iyar Democrat da Donald Trump na jam’iyar Republican sun samu nasarar karfafa samun jam’iyun su su tsayar da su yan takarar shugaba, a yayinda suka lashe muhimmancin jihohi a zaben gandu na fidda yan takara da aka yi jiya Talata da ake cewa Super Tuesday, a zamar ranar mafi muhimmanci a zaben na tsayar da dan takara.
Yau Talata ne ake zaben Gandu a Amurka, wanda ake kira Super Tuesday a turance, inda za a gudanar da zaben jihohi 12 da ya kasance ranar zabe mafi girma cikin wata guda.
‘Yan takarar shugaban kasar Amurka su biyu da suka hada da tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton da Sanata Banie Sanders sun tafka muhawara a daren jija a birnin Milwuaukee na jihar Winscosin, yayin da salon yakin shiga fadar White House ya dauki sabon salo.
‘Yan takarar shugaban cin Amurka Sanata Banie Sanders shi da mashahurin mai kudin nan Donald Trump, sun samu gagarumar nasara a cikin jamiyyun su a zaben da akayi a jihar New Hamspshire.
Dan siyasar mai ra’ayin sassauci na jam’iyyar Democrat Sanata Bernie Sanders da kuma dan baro-baro Donald Trump na jam’iyyar Republican da suke neman shugabancin Amurka, sun sami lashe zaben fidda gwanin da aka yi a New Hamshire bayan gama na Iowa a makon da ya gabata.
‘Yan takarar neman shugabancin Amurka a karkashin Jam’iyar Republican sun tafka muhawara a New Hampshire, wacce ta fi maida hankali kan harkokin kasashen waje, inda suka yi ta sukar junansu a daren jiya Asabar.
Domin Kari