Hillary ita ta biyo bayan Bernie da kaso 39 cikin 100 bisa kaso 60 cikin 100 da dattijon ya samu. Shi kuma Gwamnan Ohio John Kasich ya biyo bayan Trump da kaso 16 cikin 100 da kaso 35 cikin 100 da attajirin ya samu.
Tuni dama dai kafofin yada labarai suka yi kintacen samun nasarar wadannan mutane a New Hamshire.
Attajiri Trump ya jaddadawa masoyansa cewa suna kan bakansu na sai sun sake mikar da Amurka tsaye kamar yadda take a da. Shi kuwa dattijon garin Vermont Sanata Sanders ya tsaya bisa maganarsa ta cike wagegen gibin rashin daidaiton tattalin arzikin kasa tsakanin al’ummar Amurka.
Masana siyasa sun ce kada mage dai ba yanka ba, domin kuwa akwai sauran zaben fidda gwanayen bayan wannan.