Ba za a sanar da ita a matsayin ‘yar takarar shugaban kasar jam’iyar Democrat ba sai lokacin babban taron jam’iyar da za a gudanar watan gobe, sai dai ta sami wakilai dubu biyu da dari uku da tamanin da uku da take bukata na kada dan majalisar dattijai mai wakiltar jihar Vermont Bernie Sander.
John Hudak, mataimakin darektan cibiyar kula da harkokin mu’amala da jama’a na makarantar Brookings, ya shaidawa Muryar Amurka, cewa, ba a maida hankali kan muhimmancin nasarar da ta samu dalili da Clinton ta riga tayi fice, kuma an nuna mata goyon baya tun lokacin da ta shiga takara.
Yace, abin mamaki ne a wannan lokacin na tarihi inda mace ta zama ‘yar takarar jam’iya karon farko, amma ake ganinshi kamar abinda aka sa ran zai faru kawai. Yace duk da haka, ina gani, zata kara bayyana kowacce irin ‘yar takara ce ita, da kuma tarihin da tayi yayinda ta shiga yakin neman zabe gadan gadan.
Clinton tayi taka tsantsan jiya litinin da dare, da cewa, duk da yake rahotannin kafofin yada labarai sun nuna ta sami galaba, har yanzu akwai jihohi shida da ake gudanar da zabe yau Talata, tana kuma yaki tukuru domin ganin ta lashe dukan kuri’un.
Kakakin Sanders Micheal Briggs ya fitar da sanarwa cewa, kafofin sadarwa suna riga mallam masallaci wajen tsaida Clinton, yace tana ikirarin samun rinjaye ne kawai idan aka kirga wakilan da suke goyon bayanta a halin yanzu, da zasu iya canza ra’ayinsu kafin lokacin babban taron jam’iyar na kasa.
Sandar yaci alwashin ci gaba da yakin neman zabe har zuwa karshe, wani abinda Hudak yace, hanya ce ta ci gaba da tsima magoya bayansa har zuwa lokacin da zai janye.