Dan takarar shugabancin Amurka karkashin jamiyyar Republican Donald Trump wanda ya kwashe sati guda yana cece kuce akan batun Khizr da Ghazala Khan, iyayen wani sojan Amurka da aka kashe a Iraqi, ya janyo wasu ‘yan jamiyyar tasu ta Republican fitowa fili suna sukar dan takarar nasu.
Caccakar da dan takarar shugaban kasar Amurka karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump ya ke sha, ta kara tsanani jiya Talata, saboda sukar wani iyalin Musulmin Amurka wadanda dan su ya mutu yayin da ya ke yaki ma Amurka a Iraki a 2004.
Cacar baki tsakanin dan takarar shugabancin Amurka Donald Trump da mahaifin wani sojan Amurka musulmi da dan kunar bakin wake ya kashe a Iraqi a 2004, shine ya mamaye yakin neman zaben shugabancin Amurka a jiya Litinin.
Mahaifin sojan Amurka nan Captain Humayun Khan, yayi kira ga Shugabannin Jamiyyar Republican da su ja kunnen dan takarar shugaban kasar su Donald Trump daya daina anfani da sunan dan sa, wurin kamfe domin da yawan mutane zasu kalli hakan a matsayin kaskantarwa ga dan nasa, wanda ya sadaukar da rayuwar sa wurin gudanar da aikin kasa.
Bayan da aka kammala manyan turakan jam’iyyun siyasa a Amurka, yanzu hankula za su karkata ne akan ‘yan takarar da jami’yyun suka fitar, wato Donald Trump a karkashin jam’iyyar Republican da kuma Hillary Clinton a bangaren jam’iyyar Democrat.
A daren jiya Alhamis ne ‘yar takarar shugaban kasa a karkashin tutar jam'iyyar Democrat Hillary Clinton, ta yi jawabin amincewa da zama ‘yar takarar jam'iyyar su ta Democrat, a cikin jawabin nata ta bukaci Amurkawa su hada kai domin fuskantar kalubalen dake gaban kasar.
Jam’iyyar Democrat ta tabbatar da tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, a matsayin ‘yar takarar neman shugabancin Amurka karkashin tutar jam’iyyar, wanda hakan yasa ta zama mace ta farko da ta taba zama ‘yar takarar ‘daya daga cikin manyan jam’iyyun kasar, a yakin neman shugabancin Amurka.
Jiya Litinin ne jam'iyyar Democrat ta bude babban taronta na wanaki hudu a birnin Philadelphia dake gabashin Amurka, a kokarinda take yi na nuna kan jam'iyyar a hade yake, a dai dai lokacinda jam'iyyar take fuskantar rikici sakamakon sakonni emails da aka fallasa.
A jiya Lahadi shugabar jam’iyyar Democrat ta nan Amurka tayi murabus, yayin da jam’iyyar za ta yi babban taron ta a yau Litinin domin tabbatar da tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton a matsayin ‘yar takarar shugabancin kasa a zabe mai zuwa.
Kwana guda bayan da dan takarar jam’iyar Republican, Donald Trump, ya sha alwashin gina Katanga tsakanin Amurka da Mexico, shugaban kasar Mexicon, Enrique Pena Nieto, na ziyara a Amurkan a yau Juma’a.
Gwamnan Jihar Indiana Micheal Pence, ‘dan ra’ayin rikau na jamiyyar Republican, wanda shine Donald Trump ya zaba a matsayin wanda zai zama mataimakin shugaban kasa, a jiya Talata ya bayar da dalilan da yasa yake ganin sune suka dace su jagoranci Amurka.
Jam'iyyar Republican ta ayyana hamshakin dan kasuwan nan mai harkar gine-gine Donald Trump, a matsayin dan takararta na Shugaban kasa a hukumance, a zaben da za a yi wannan shekarar ta 2016.
Domin Kari