Tsohuwar ‘yar takarar shugaban kasa a Jami’yar Green Party a nan Amurka, Jill Stein, ta ce za ta dangana da kotun tarayya, a kokarin da ta ke yi na ganin an sake kidaya kuri’un Jihar Pennsylvania na zaben shugaban kasar da aka yi.
Wani alkali a nan Amurka ya shawarci zababben shugaban kasa da ya tabbatar ya kammala shara’ar almundahanar dake gaban sa na game jami’ar sa.
Dubun dubatan mutane a birnin New York dake gabashin Amurka, zuwa jihar California a dake Yamma sun cika manya-manyan tituna, yau suka shiga rana ta uku ta nuna kyamar su ga zaben Donald Trump a matsayin shugaban Amurka na 45.
A wani gefen kuma...wasu mutanen babbar jihar nan ta California, wadanda suka jefa wa Hillary Clinton kuri’u masu yawan gaske, sun fara barazanar fitar da jihar tasu daga cikin Amurka don su nuna cewa basa kaunar Donald Trump ya zamar musu shugaban kasa.
Dubban mutane a biranen Amurka daban-daban, kama daga New York har zuwa jihar California, su na ci gaba da fitowa kan tituna suna gudanarda gagarumar zanga-zagar nuna rashin yardarsu da zaben da aka yi wa Donald Trump a matasyin sabon shugaban Amurka na 45 a zaben da aka gudanar ranar talatar da ta gabata.
Shugaban Amurka Barack Obama ya gana da sabon zababben shugaba Donald Trump a fadar White House.
Dubban jama’a dauke da kwalayen dake yin tur da zababben shugaban Amurka Donald Trump sun yi zanga zanga.
A halin yanzu kuma, mutanen kasar Kenya inda iyalan shugaban Amurka mai ci yanzu Barrack Obama suka samo asali, mutane da dama ne suka kyautata zaton Hillary Clinton ce za’a zaba don ta ci gaba da ayyukan dan’uwan nasu ya fara.
Yar takarar shugabancin kasar Amurka a karkashin lemar jami’iyar Democrats Hillary Cliunton ta bayyana amincewarta da sakamakon zaben da aka kamalla a ranar Talatar shekaranjiya inda ta taya wanda aka zaba din Donald Trump na Republican, kuma ta yi mishi fatar samun nasara a jagorancin da zai yiwa Amurkawa.
Gwamnatin kasar Nijar ta taya Amurka da amurkawa murnar gudanar da zaben shugaban kasa tare da samun sabon shugaban kasa wanda yanzu yake jiran gado
Kamar kasar Kamaru nasarar Donald Trump a zaben shugabancin kasar Amurka bata yiwa al'ummar kasar dadi ba saboda kyamar musulmi da ya keyi kamar yadda ya furta yayinda yake fafutikar neman zabe
Domin Kari