Democrat na da tazara kan abokin karawarta Donald Trump na jam’iyyar Republican, duk kuwa da yake Amurkawa na ganin ‘yan takarar biyu a matsayin marasa farin jini.
Ita dai Clinton, wadda take tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka ce, na neman zama mace ta farko da zata zama shugabar Amurka, yanzu haka ta baiwa abokin karawarta ‘dan jam’iyyar Republican wanda yake hamshakin mai kudi kuma shararren mai sayar da gidaje tazara daga kaso 4 zuwa 7 cikin 100, wanda kuma a wannan makon ake sa ran za a tsayar da shi ‘dan takara a birnin Cleveland na jihar Ohio.
Zaben jin ra’ayin da kamfanin labaru na ABC news da Washington Post suka gudanar ya nuna Clinton na gaba da kaso 47 zuwa 43 cikin 100. Su kuma sauran kafofin yada labaran da suka da NBC News da Wall Street Jounal nasu zaben ya nuna Clinton na gaba da kaso 47 zuwa 41. Sai kuma CNN da ORC Internation wanda nasu ya nuna tana gaba da kaso 49 zuwa 42.