A yau Litinin aka bude babban taron Jam'iyyar Republican a birnin Cleveland da ke jihar Ohio inda taron zai fi maida hankali kan batutuwan tsaron kasa da baki.
Daga cikin wadanda za su yi jawabi akwai tsohon gwamnan jihar Texas, Rick Perry, da mahaifiyar wani Ba’amurke da aka kashe a Benghazi da ke Libya, da masu fafutukar neman a samar da sauye-sauye a fannin shige da fice a kasar, da tsohon Magajin Garin New York, Rudy Guiliani da kuma uwargidan Trump Melania.
A wata hira da gidan talbijin na CBS ya nuna mai taken 60 Minutes a ranar Lahadi, Trump ya amsa wata tambaya kan halin da duniya ke ciki, wacce ake ganin somin-tabi ce dangane da irin caccakar da shugaba Barack Oabma da ‘yar takarar Democrat Hillary Clinton za su sha a wannan mako.
A baya, Trump ya ba da shawarar gina wata Katanga a kan iyakar Amurka da Mexico da kuma hana musulmi shiga kasar, koda ya ke a hirar ta jiya Lahadi, ya dan sassauta matsayarsa kan hana musulmi shiga Amurka, inda ya ce a fi maida hankali kan kasashen da mutane suka fito.