Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun San Za'a Kai Hari Cibok


Kakakin Ma'aikatar Tsaron Najeriya, Chris Olukolade wanda fitar da sanarwar ceto kusan duka daliban Chibok, daga baya kuma ya janye kalaman.
Kakakin Ma'aikatar Tsaron Najeriya, Chris Olukolade wanda fitar da sanarwar ceto kusan duka daliban Chibok, daga baya kuma ya janye kalaman.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International tace shaidu da ta tattara sun bayyana cewa dakarun tsaron Najeriya sun san cewa ‘yan bindiga sun doshi garin Cibok a daren 14 ga watan Afrilu, amma suka kasa daukar matakin yin rigakafi, duk da gargadin da suka samu.

Darektan bincike game da Afirka na kungiyar, Netsanet Belay, yace ganin cewa sojoji sun san cewa za a kai wannan harin amma ba su dauki matakan hanawa ba, yin watsi da nauyin dake wuyarsu na kare fararen hula ne, wadanda ke fuskantar irin wadannna hare-hare. Yace tilas shugabannin Najeriya suyi amfani da dukkan halaltattun hanyoyi na tabbatar da cewa irin wannan bai sake faruwa ba.

Kungiyar Amnesty ta ce ta tabbatar ta hanyoyi da dama cewa tun karfe 7 na maraicen 14 Afrilu, hedkwatar sojoji dake Maiduguri, da kuma rundnar sojan dake garin Damboa, kilomita 37 daga Chibok, sun samu labari daga majiyoyi da yawa cewa ga 'yan bindiga sun doshi garin Chibok. Wasu manyan hafsoshin sojan Najeriya biyu sun gaskata wannan labarin in ji Amnesty.

Amma sai aka bar sojoji kwaya 17 dake Chibok kawai da 'yan sandan garin suka yi fada da wadannan 'yan bindiga ba a kai musu dauki ba. Su kuma da aka fi karfinsu, suka ja da baya.

A kwanakin baya, wani sojan Najeriya wanda ya tattauna da Sashen Hausa na Muryar Amurka, ya zargi da hannun manyan sojoji a hare-hare da ake ta kaiwa a arewa maso gabashin Najeriya, inda ma yace akwai sojojin Najeriya dake yiwa Boko Haram aiki, suna kashe 'yan uwansu sojoji.
XS
SM
MD
LG