Daga karshe dai Hamas ta bayar da sunayen, kuma Isira’ila ta ce za a fara tsagaita wuta da karfe 11:15 na safe.
An kama Seyni Amadou, babban editan gidan talabijin na Canal 4, in ji kungiyar CAP-Medias-Niger, mai wakiltar ma'aikatan yada labarai a kasar. A ranar Juma'ar da ta gabata ma'aikatar sadarwa ta Nijar ta sanar da dakatar da tashar ta shi na tsawon wata guda.
Majalisar zartarwar Isra’ila ta tabbatar da wata yarjejeniyar tsagaita wuta da sanyin safiyar yau Asabar a Gaza da kuma sakin mutanen da ake garkuwa da su domin kawo karshen yaki da Hamas na watanni 15.
Za a rantsar da Donald Trump da zababben matamakin shugaban kasa kan mukamansu a cikin babban dakin taro na Majalisar Dokokin Amurka.
Ana sa ran kungiyar Hamas ta saki kashin farko na mutane da take rike da su karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza a Lahadi mai zuwa, kamar yadda ofishin Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana a yau Juma’a, bayan shafe watani 15 ana gwabza yakin da ya daidaita zirin
An samu wadanda ake zargin da tsabar kudi dalar Amurka dubu 400 da wani adadi na Gwal, abinda da ya daga hankali, kan irin gagarumar ta’asar da suke yi.
Wasu mambobi 2 na tsagin siyasa na Hamas sun yi watsi da sanarwar da ta fito daga ofishin Firai Ministan Isra’ila Benyamin Netanyahu da ke cewa kungiyar na sake tattaunawa a kan wasu bangarori na yarjejeniyar.
A makon da ya gabata, ayarin fiye da jami’o’in Jamus 60 suka bayyana cewa sun juyawa dandalin baya.
Kulla wannan yarjejeniya na zuwa ne yayin da yakin na Isra'ila da Hamas ya haura wata 15 da barkewa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press ya samu kwafin yarjejeniyar da aka tsara, sannan wani jami'in Masar da wani jami'in Hamas sun tabbatar da ingancinsa.
Kasashen EU 6 sun bukaci kungiyar ta sassautawa Syria takunkuman da ta kakaba mata a fannonin sufuri da makamashi da harkar banki na wani dan lokaci, a cewar sanarwar da kamfanin dillancin labaran Reuters ya gano.
Sabon shugaban Syria Ahmed al-Sharaa ya ce yana fatan ganin wata sabuwar alakar dangantaka da Lebanon, kwanaki bayan kasar Lebanon mai fama da rikici ta zabi shugaban kasa a wannan makon, bayan shafe shekaru biyu ana takun saka.
Domin Kari
No media source currently available