Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kotu A Kasar Congo Ta Daure Yan Kasar China A Gidan Kaso

Yan kasar Sin da aka kama a Jamhuriyar Democradiyyar Congo
Yan kasar Sin da aka kama a Jamhuriyar Democradiyyar Congo

An samu wadanda ake zargin da tsabar kudi dalar Amurka dubu 400 da wani adadi na Gwal, abinda da ya daga hankali, kan irin gagarumar ta’asar da suke yi.

Wata kotu a jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ta daure wasu yan kasar China su 3, shekaru uku uku a gidan kaso, bisa aiyyukan hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.

Kotun dake garin Bukawu babban birnin kasar dake yankin gabashin kasar ta Congo mai cike da arzikin Gwal, a yankin kudancin Kivu, ta aika da mutanen gidan kaso ne da yammacin Talata, sakamakon samun su da laifuffukan saye da hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, safarar kudi da sauran laifuffuka.

An samu wadanda ake zargin da tsabar kudi dalar Amurka dubu 400 da wani adadi na Gwal, abinda da ya daga hankali, kan irin gagarumar ta’asar da suke yi.

Da yake Magana da manema labarai, gwamnan yankin Kivu ta kudu, Jean Jacque Purusi, yace, mutanen yankin sun gaji da irin wadannan mutanen dake wandaka da arzikin kasar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG