An samu wadanda ake zargin da tsabar kudi dalar Amurka dubu 400 da wani adadi na Gwal, abinda da ya daga hankali, kan irin gagarumar ta’asar da suke yi.
Wasu mambobi 2 na tsagin siyasa na Hamas sun yi watsi da sanarwar da ta fito daga ofishin Firai Ministan Isra’ila Benyamin Netanyahu da ke cewa kungiyar na sake tattaunawa a kan wasu bangarori na yarjejeniyar.
A makon da ya gabata, ayarin fiye da jami’o’in Jamus 60 suka bayyana cewa sun juyawa dandalin baya.
Kulla wannan yarjejeniya na zuwa ne yayin da yakin na Isra'ila da Hamas ya haura wata 15 da barkewa.
Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press ya samu kwafin yarjejeniyar da aka tsara, sannan wani jami'in Masar da wani jami'in Hamas sun tabbatar da ingancinsa.
Kasashen EU 6 sun bukaci kungiyar ta sassautawa Syria takunkuman da ta kakaba mata a fannonin sufuri da makamashi da harkar banki na wani dan lokaci, a cewar sanarwar da kamfanin dillancin labaran Reuters ya gano.
Sabon shugaban Syria Ahmed al-Sharaa ya ce yana fatan ganin wata sabuwar alakar dangantaka da Lebanon, kwanaki bayan kasar Lebanon mai fama da rikici ta zabi shugaban kasa a wannan makon, bayan shafe shekaru biyu ana takun saka.
Binciken ya yi kiyasin cewa tsakanin watan Oktoban 2023 zuwa Yunin 2024, an sami mutuwar Falasdinawa sama da 64,000 sakamakon tashin hankali a Gaza, wanda ke nuni da cewa ma'aikatar lafiya ta Hamas da ke yankin, ta rage a rahoton adadin da ta bayar na wadanda suka mutu da kusan kashi 41%.
"Batun da za mu yi musu shi ne cewa, matsayin Amurka a yankin na da matukar karfi a yanzu," in ji Sullivan, a yayin da ya ke amsa tambayar Muryar Amurka a wani taron tattaunawa da 'yan jarida a jiya Juma'a.
“Babu yadda za mu taba amincewa da kai harin bam kan fararen hula,” a cewar Fafaroman a wani jawabin da wani hadiminsa ya gabatar a madadinsa.
Amb. Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa, gwamnatin Najeriya za ta hada gwiwa da kasar China wajen fara kera makaman yaki na matsalolin tsaro cikin gida a maimakon a ci gaba da shigowa da su sakamakon wasu matsalolin da ake fama da su wajen sayowa daga waje
China na ci gaba da kokarin abota da kasashen Afurka saboda arzikin ma'adinai da nahiyar ke da shi.
Domin Kari
No media source currently available