Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hamas Ta Musanta Zargin Ja Da Baya Kan Yarjejeniyar Tsagaita Wuta

Wasu mambobi 2 na tsagin siyasa na Hamas sun yi watsi da sanarwar da ta fito daga ofishin Firai Ministan Isra’ila Benyamin Netanyahu da ke cewa kungiyar na sake tattaunawa a kan wasu bangarori na yarjejeniyar.

Shugabannin Hamas 2 sun yi fatali da zarge-zargen Isra’ila na cewar kungiyar ‘yan gwagwarmayar Falasdinawan na ja da baya a kan wasu bangarori na yarjejeniyar tsagaita wuta da sakin mutanen da ake garkuwa da su a Gaza da aka sanar a jiya, Laraba.

Kafafen yada labaran Isra’ila sun ce me yiyuwa gwamnatin ta samu tsaiko a kan batun amincewa da wasu bangarori na yarjejeniyar saboda sabanin ra’ayin da aka samu a cikin kawancen jam’iyyun da ke mulkin kasar.

Wasu mambobi 2 na tsagin siyasa na Hamas sun yi watsi da sanarwar da ta fito daga ofishin Firai Ministan Isra’ila Benyamin Netanyahu da ke cewa kungiyar na sake tattaunawa a kan wasu bangarori na yarjejeniyar.

“Babu wata hujja game da ikirarin Netanyahu na cewa kungiyar na ja da baya a kan wasu bangrori na yarjejeniyar tsagaita wuta,” kamar yadda jami’in Hamas Sami Abu Zuhri ya shaidawa AFP.

Ofishin Netanyahu ya ce har yanzu ana tattaunawa a kan bayanan karshe na yarjejeniyar kuma Firai Ministan ba zai ce komai ba har sai an amince da dukkanin bangarorinta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG