“Babu yadda za mu taba amincewa da kai harin bam kan fararen hula,” a cewar Fafaroman a wani jawabin da wani hadiminsa ya gabatar a madadinsa.
Amb. Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa, gwamnatin Najeriya za ta hada gwiwa da kasar China wajen fara kera makaman yaki na matsalolin tsaro cikin gida a maimakon a ci gaba da shigowa da su sakamakon wasu matsalolin da ake fama da su wajen sayowa daga waje
China na ci gaba da kokarin abota da kasashen Afurka saboda arzikin ma'adinai da nahiyar ke da shi.
Koriya Ta Arewa ta sake gargadi game da ingancin sabbin makamanta.
Chadi da Senegal sun maida martani da kakausan murya bayan da Shugaba Macron ya bayyana cewa Faransa ce ta yi niyar kwashe sojojinta daga Afirka sabanin yadda ake ta shailar cewa korarsu aka yi daga nahiyar
Wata girgizar kasa mai karfin gaske ta girgiza yankin yammacin China mai yawan tsaunuka da wasu sassa na kasar Nepal a yau Talata, inda ta lallata daruruwan gidaje tare da cika tituna da baraguzan duwatsu da kuma hallaka akalla mutane 95 a yankin Tibet.
Babban Hafsan Sojin Isra’ila ya kai ziyara inda aka kai wani mummunan harin bindiga akan wata motar safa dauke da Yahudawa a yankin yammacin kogin Jordan a jiya Litinin, ya kuma sha alwashin gano wadanda suka kai harin.
Za a dorawa sabon shugaban jam’iyyar Liberal din alhakin nema mata karin goyon baya gabanin babban zaben kasar da wajibi a gudanar da shi a cikin shekarar da muke ciki.
Yawan shari’un da Sarkozy yake fuskanta sun dishashe shekarun da ya kwashe yana aiki tun bayan da ya fadi zabe a 2012. Sai dai kuma har yanzu ya ci gaba da kasancewa madubin duba ga mutane da dama sannan sanin kowa ne cewa yana yawan ganawa da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron a kai akai.
Gwamnatin kasar ta ayyana zaman makoki na kwanaki hudu a hukumance. Za’a yi wa Simitis jana’izar girmamawa ta kasa.
Kungiyar ba da agaji ta Red Crescent ta Falasdinawa ta ce samamen ya fara ne da daren Juma’a kuma ya haifar da arangama mai tsanani.
Shugabar gwamnatin rikon kwarya ta Haiti, Leslie Voltaire, tare da Firayim Minista Alix Didier Fils-Aime da jakadan Amurka Dennis Hankins, sun yi maraba da sojojin a filin jirgin saman Port-au-Prince,
Domin Kari
No media source currently available