Da farko za'a fara zaben sabon kakaki, inda mutumin da ke kan kujerar Mike Johnson, ke fafutukar ci gaba da zama a kanta.
Har yanzu ana ci gaba da neman fasinjojin daka iya bata, a cewar hukumar tsaron kasar Tunisia, wacce ke kula da gabar ruwan kasar.
A yau Alhamis, Fafaroma Francis ya bayyana ta'aziyarsa ga babban limamin katolika na New Orleans akan harin da aka kai birnin dake Amurka wanda ya hallaka akalla mutane 15, a cikin sakon da fadarsa ta Vatican ta aike.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya aike da sakon ta'aziyarsa ga iyalan mutanen da mummunan harin da aka kai da mota kan dandazon masu bikin shigowar sabuwar shekara ya rutsa dasu a birnin New Orleans a yau Laraba.
Zababben shugaban ya wallafa hakan a shafinsa na sada zumunta gabanin a fayyace bayanan mutumin da ya kai harin a matsayin ba-Amurke mai suna Shamsud-Din Jabbar,
Wanda ake zargin ya hallaka akalla mutane 10 tare da jikkata 30 gabanin a harbe shi a musayar wuta da 'yan sanda.
Hukumomi a birnin New Orleans na Amurka sun bayyana cewa mutane 10 sun mutu kuma fiye da 30 sun jikkata sa'ilin da wata mota ta afka cikin dandazon jama'ar dake kan titin Bourbon.
An zartarwa Iraniyawan hukuncin kisan ne a yankin Dammam dake gabar tekun Fasha na masarautar, saboda samunsu da laifin fataucin ganyen tabar wiwi cikin Saudiyya.
Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta shawarci ‘yan kasar da ke shirin tafiya zuwa kasar Australia da su sani cewa akwai biranen kasar dake fama da tabarbarewar tsaro.
Shekarar 2024 ta kasance shekara mai cike da abubuwan tarihi, inda aka samu muhimman labarai da suka shafi siyasa, tattalin arziki, rikice-rikice, da al’amuran jin kai. Munyi duba kan wasu daga cikin manyan labarai da suka fi daukar hankali a shekarar 2024.
A yayin da ake ci gaba da nuna alhini ga mutuwar tsohon shugaban kasar Amurka Jimmy Carter, wanda ya rasu yana da shekara 100 a duniya
Shugaba Yoon ya dakatar da mulkin farar hula na dan wani lokaci a ranar 3 ga watan Disamban 2024, inda ya jefa kasar cikin mafi munin rikicin siyasar da ta jima ba ta ga irinsa ba.
Domin Kari
No media source currently available