Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Yanke Wa Wani Dan Koriya Ta Kudu Hukuncin Daurin Rai Da Rai Bisa Laifin Daba Wa Wani Wuka


Wani Dan Koriya Ta Kudu Da Ya Daba Wa Wani Wuka
Wani Dan Koriya Ta Kudu Da Ya Daba Wa Wani Wuka

Kamfanin dillancin labarai na Yonhap ya bayar da rahoton cewa, a ranar Laraba ne wata kotu a Koriya ta Kudu ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga mutumin da ya kashe mutum daya tare da jikkata wasu uku a wani hari da aka kai a birnin Seoul a bara.

Kotun ta bayyana harin da Cho Seon ya kai ga mutanen da bai san su ba a watan Yulin bara a matsayin "mummunan zalunci" yayin da ta yanke hukuncin, a cewar Yonhap.

Shaidun gani da ido a lokacin sun bayyana abubuwan firgita da suka faru yayin da Seon ya zaro wuka a wajen wata tashar jirgin karkashin kasa ya daba wa wani mutum a bayansa sau da yawa kafin ya gudu ya kai wani harin ga wasu karin mutane.

"Abin da ya dace kawai shi ne a hana wanda ake karar 'yanci da walwala... a kuma ware shi daga cikin jama'a har abada don kiyaye lafiyar jama'a," in ji kotun.

Wani Dan Koriya Ta Kudu Da Ya Daba Wa Wani Wuka
Wani Dan Koriya Ta Kudu Da Ya Daba Wa Wani Wuka

Tun da farko dai masu gabatar da kara sun nemi hukuncin kisa ga maharin.

Makwanni biyu kacal bayan harin na watan Yuli, an kai wani hari na biyu kan jama'a, lokacin da wani mutum ya tuka mota a kan hanyar tafiyar jama'a kafin ya far wa mutane a wani kantin sayar da kayayyaki a Seoul, inda ya kashe mutane biyu.

Lamarin guda biyu sun sa shugaba Yoon Suk Yeol, wanda tsohon babban mai shigar da kara ne, yin kira da a hada karfi da karfe, inda ‘yan sanda kuma suka bayyana cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen amfani da makamai.

Ana ɗaukar Koriya ta Kudu a matsayin ƙasa mai aminci sosai, tare da adadin kisan kai 1.3 kacal a cikin mutane 100,000, a cewar bayanan gwamnati na baya-bayan nan.

Sai dai baya ga ci gaba da kai hare-haren wuka, an kai wa wasu 'yan siyasa hari a bainar jama'a, ciki har da jagoran 'yan adawa Lee Jae-myung, wanda aka caka masa wuka a wuya a farkon wannan watan.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG