Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Birtaniya Ta Tasa Keyar Akalla 'Yan Najeriya Da Ghana 44


Hotunan wasu yan ci rani da aka dawo dasu Nijer
Hotunan wasu yan ci rani da aka dawo dasu Nijer

Yan Najeriya da wasu 'yan Ghana kimanin arba’in da hudu aka mayar kasashensu na asali bayan da aka samesu da laifin zama ba bisa ka’ida ba a Britaniya.

Jaridar Guardian da ake bugawa a kasar ta Birtaniya ta bayyana damuwa a game da yanayin da ta ce ta sami 'yan ciranin da suka shigo kasar neman rayuwa mai inganci a gabanin a mayar da su kasashensu, inda ta tattauna da wani da yayi yunkurin halaka kansa da wani da ya bayyana cewa ya zauna a Ingila na tsawon shekaru 15, amma duk da haka ba a amince da shaidar neman mafakarsa ba, lamarin da ya bayyana a matsayin tsagwaron rashin adalci.

Tun bayan da jam’iyyar Labour ta hau karagar mulki a watan Yulin da ya gabata, an fitar da 'yan cirani kimanin dubu uku da dari shida da suka fito daga kasashe daban-daban bayan da yunkurinsu na neman mafaka ya ci tura.

Gwamnatin Britaniyan dai ta sha alwashin ci gaba da korar bakin da suka zame mata alakakai a kasa.

Saurari cikakken rahoton Ramatu Garba:

Birtaniya Ta Tasa Keyar Akalla 'Yan Najeriya Da Ghana 44
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG