Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar yayi tir da karramawar sojin da aka yiwa Seyi Tinubu da ga Shugaba Bola Tinubu, inda ya bayyana hakan da zubar da mutuncin dadaddiyar al’adar rundunar sojin Najeriya.
Ya bukaci a gaggauta gudanar da bincike a kan lamarin, wanda ya bayyana da ganiyar keta doka da tsari.
Sanarwar da ofishin yada labaransa ya fitara jiya Lahadi, dauke da sa hannun mashawarcinsa akan harkokin yada labarai, Paul Ibe, Atiku ya soki lamirin faifan bidiyon dake nuna yadda wata kungiya da aka bayyana da gamayyar sojojin dake samun horo ta Najeriya (Nigerian Cadet Network) ke karrama Seyi Tinubu da faretin ban girma a hukumance.
Ya kara da cewa an ware irin wannan karramawa ce ga fitattun jami’an gwamnati sannan ya zargi kungiyar da yin zagon kasa ga mutuncin rundunar sojin Najeriya.
Atiku ya kuma tuhumi sahihancin gamayyar ta “Nigeria Cadet Network”, inda yace binciken farko da aka gudanar ya nuna cewar bata cikin bangarorin rundunar sojin Najeriya da aka sani.
Ya kuma bayyana damuwa akan yadda kungiyar ke amfani da bindigogi, musamman a wannan lokaci da kasar ke yaki da yaduwar haramtattun makamai.
Dandalin Mu Tattauna