A daidai lokacin da Majalisar Wakliai ta amince da yin bincike kan rugujewar tashar watar lantarki da ke ba jihohin Arewa wuta har na tsawon kwanaki, Kamapanin bada wuta ya ce 'yan ta'adda ne ke lalata hanyoyin bada wutar, to saidai tsohon Shugaban Kampanin Wutar Lantarki na Kaduna Alhaji Idris ya ce lallai ana bukatna bincike a wannan fanin, amma kuma ba kowa ne zai iya ba, kamar yadda za ku ji a wannan rahoto da Wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda ta hada mana.
Na’urar wutar lantarkin ya lalace har sau 8 a cikin makonni biyu da suka gabata a cewar kungiyar Shahararru masu zaman kansu wadanda aka fi sanin da OPS ko kuma Organised Private Sector da turanci.
Kungiyar OPS ta ce a baya bayan nan an samu rugujewar wutar lantarki har sau 105 tsakanin Gwamnatin baya da wannan Gwamnatin, karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun Shugaban Sashin wayar da kan al'umma na Kampanonin TCN Ndidi Mba ya ce rugujewar wutar ta fi shafan Arewa ta tsakiya da Arewa ta Yamma da kuma Arewa ta Gabas kuma yan tá'adda ne ke lalata hanyoyin samar da wutar.
Shugaban Kwamitin Kula da hidimar jama'a a Majalisar Wakilan Najeriya Injiniya Sani Umar Bala ya yi bayani akan abin da ya ce shi ya sa Arewcin kasar ta tsinci kanta cikin duhu har tsawon kwanaki sannan, ya kara da bayanin cewa tsakanin tashar samar da wuta ta Shiroro a Jihar Neja da Kaduna, an ruguza (lallata) turakun lantarki guda biyu da suke da karfin megawatt 330.
Sannan ita ce ta ke baiwa shiyoyi uku na Arewacin Najeriya wuta har da wani sashi na Kasar Njar. Injiniya Sani ya ce kamata yayi gwamnati ta dau matakan tsaro don kare dukanin turakun wutar lantarki a kasar.
A saurari sautin rahoton Madina Dauda:
Dandalin Mu Tattauna