Ambasadan Amurka a Nijeriya, James Entwistle, ya tabbatar da dalilin da yasa Amurka ba zata dena bada taimako ga kasar domin cutar kanjamau ba ko da yake ya yarda cewa dokar Najeriya ta hana auren jinsi daya, ‘wata babbar damuwa ce.’
Najeriya ta sake yin yunkurin kafa dokar da ta shafi shan taba, wani yunkuri da cikin shekaru masu zuwa zai iya ceton rayukan milyoyin matasan Najeriya daga cututtuka da kuma mutuwar dake da dangantaka da shan taba.
Shugabar masu lalurar shan inna ta Jihar Kano, Amina Abdullahi Getso, ta ce wayar da kan na da kyau, amma ana bukatar gyara kan yadda masu unguwanni ke ba iyalansu aikin rigakafin.
Shugaban kungiyar masu fama da cutar shan inna na kasa, Aminu Ahmed Tudun Wada, yace hannu day aba ya daukar jinka.
Ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Bauchi (PHCDA) ta sami mutane uku da suke sa zaton sun kamu da ciwon kwalara.
Darektar kiwon lafiya a yankin, Hjiya Amina Jibril, ta ce wannan lamarin ya faru ne a gundumomi 11 na karamar hukumar Ilela.
Har yanzu ana samun yaran da kan rasa rayukansu a baban asibitin Maradi a jamuhuriyan Nijar, a sakamakon cutar zazzabin cizon sauro.
Hawan jinni ya fara zama wata babbar kalubala ga lafiya. Hawan jinni wani yanayi ne inda karfin bugun jinni a cikin jijioyin jinni yake hawa fiye da yada ya kamata.
An kawas da wani maganin kiyaye kwayar cutar kanjamau da ake yi a Nijeriya daga kasuwa sakamakon rashin inganci bayan marasa lafiya sun mutu bayan sun fara shan maganin.
Rashin aiki kamar yadda ya kamata, da kuma wasu batutuwan gudanar da aiki sun sa an tura sabbin ma’aikatan kiwon lafiya a wasu kananan hukumomin Jihar Kano don karfafa yaki da Polio
Jami'an hukumar kiwon lafiya ta duniya da na jihar Bauchi sun gudanar da aikin a bayan da aka gano cewa an tsallake wasu yara a kyamfe na baya
Masanan kimiyya dake kokarin nemo maganin da zai warkar da cutar kanjamau sun ce koma bayan da aka samu wajen mutane biyun da ake tsammani sun warke daga kanjamau ya kara masu kaimi ne maimaikon ya karya masu gwiwa.
Domin Kari
No media source currently available
Wani kamfnin wasan bidiyo ya kaddamar da wani wasa da nufin karfafawa maza masu jinni a jika guiwa, su motsa jiki a wannan yanayin da ake fama da annoba da nufin taimakawa a rage gallazawa mata.
An yi kiyasin cewa, kimanin kashi 8% na al’ummar duniya ba su cin nama kwata-kwata. Masu kula da lamura sun ce, irin wannan rayuwar na iya zama da kalubale a kasashen nafiyar Afirka inda ake yawan cin nama da kuma kifi a galibin abincin da aka saba da shi.
Madina Shettima Pindar, kwararrar mai kula da abinda ya shafi cin abinci mai gina jiki a asibitin kwararru na birnin Maiduguri, jihar Borno a Najeriya, ta yi karin haske kan tasirin cin abinci ba nama.
Har yanzu ana cikin duhu dangane da sabon nau’in annobar COVID 19 Omicron, da ya hada da tasirin rigakafin COVID-19 da kuma, ko akwai bukatar samar da wani maganin rigakafi.