Wannan yana kunshe a cikin bayanin da jami’an kiwon lafiyar jihar suka gabatar a zauren taron da Muryar Amurka da Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Amurka, CDC, suka shirya a Kano domin nazarin hanyoyin cimma gurin kawar da cutar Polio.
Daya daga cikin wadanda suka yi bayanai a zauren taron it ace shugabar kungiyar masu lalurar shan inna ta Jihar Kano, Malama Amina Abdullahi Getso, wadda ta yi bayanin irin yadda cutar shan inna ta ke yin illa a jikin dan Adam, da irin takurarwar da ta ke yi wajen sauya rayuwa baki dayanta, ta wanda ya kamu da cutar da kuma ta iyayensa da ‘yan’uwansa.
Sannan ta koka a kan yadda masu unguwanni suke sanya sunayen iyalansu da ‘yan’uwansu a zaman wadanda zasu yi aikin bayarda maganin rigakafin, su kuma sai suje su samo wasu mutanen sun a biyansu domin su yi.
Ta ce a irin wannan yanayin, ba a gudanar da aikin yadda ya kamata domin wadanda ake bas u aikin bas u iya ba, su kuma sun a samo wadanda bas u da kwarin guiwar yin aikin tun da ba wani abin kirki zasu samu ba.
Ta bukaci fgwamnati da hukumomin kiwon lafiya da dukkan masu hannu a wannan gangami na yaki da cutar Polio da su nazarci wannan batu domin a iya cimma bukatar bayar da maganin rigakafin yadda ya kamata.