Yayinda yake bayani ga manema labarai jiya, Sakataren wannan ma’aikata, Dr Nisser Ali Umar, yace: “An sami mutane uku a Kandahar yakin yan doya cikin Karamar hukumar Bauchi wadanda ake sa zaton sun kamu da ciwon kwalara ne. Mun sami labarin cewa almajirai biyu da kuma wani mutum daya a yankin suna fama da ciwon kwalara, nan take sai muka kwashe su muka kais u asibiti inda aka basu magani an kuma sallame su. An gane cewa babu ruwan sha mai tsabta a yankin, saboda haka mun sa magni a dukan rijiyoyin yankin. Haka kuma, ma’aikatar ruwa ta jihaar Bauchi ta shiga yankin domin gyara dukan pampunan da suka fashe.”
Ya kuma kara da cewa: “Yanzu, ba mu da damuwar cutar ta kwalera amma a shirye muke domin muna kewaye da jihohi masu wannan cutar. Wannan ma’aikata ta tanada magungunan, magungunan tsabtace wurare, da kuma safar hannu ga asibitocin da suke aiki a wadannan yankunan”.
Yayi kira ga shugabannin gargajiya da kuma na addinai a jihar da su taimaka wajen wayar da kan jama’a game da tsabtace muhallin su.