Darekta mai kula da ayyukan kiwon lafiya ta yankin, Hajiya Amina Jibril, it ace ta bayyana wannan ga ‘yan jarida.
‘Yan jaridar sun sanya idanu ne a gangamin yaki da cutar shan inna na farko ckkin wannan shekara da aka yi daga ranar asabar 25 ga watan Janiru zuwa ranar talata a yankin.
Hajiya Amina Jibril ta ce jami’an da suka gudanar da wannan aiki na bayarda rigakafin da aka kamala, sun samu nasarar shawo kan iyaye 242 daga cikin wannan adadin, sun yarda sun karba.
Ta ce, “ana ci gaba da kokarin shawo kan sauran iyayen da nufin tabbatar da cewa dukkan yaran da suka cancanta daga sabbin haihuwa har zuwa masu shekaru 5, sun samu wannan kariyar.”
Darektar ta ce daga cikin yara kusan dubu 94 da aka yi niyyar ba wannan maganin rigakafin, an riga an samu nasarar bayarwa ga yara fiye da dubu 10 ya zuwa ranar asabar, ranar da aka fara wannan gangami.
A nasa bangarem, darektan ayyukan kiwon lafiya na karamar hukumar Gada a Jihar ta Sokoto, Alhaji Hassan Yabo, y ace majalisarsu ta kwaikwayi abinda karamar hukumar illela ta yi, kuma an sayi kayayyaki na was an yara domin raba wa iyaye da nufin janyo hankulansu.
Yace ya zuwa wannan lokacin ba a samu rahoton wani maihaifin da ya ki yarda a ba dansa ko diyarsa maganin rigakafin a wannan karamar hukuma ba.