Ministan kiwon lafiya na Najeriya, Onyebuchi Chukwu, ya fada a lokacin da ya kai ziyara zuwa Hukumar Kiwon Lafiya Matakin Farko ta Kasa a Abuja cewa an gano cewar ayyukan ma’aikatan da aka tura zuwa wasu yankunan kananan hukumomi na Jihar Kano, ba su wadatar kamar yadda aka zata ba.
Yace ainda suke yi yanzu shi ne tura sabbin ma’aikata domin karbar ragamar wannan aikin daga hannun wadanda aka yi imanin cewa bas u tabuka abin kirki.
Yace idan an kwatanta da wasu jihohin kasar nan ma za a ga cewa wasu yankunan kanana hukumomin Kano sun a daga cikin wadanda ke can baya.
Cibiyar Ayyukan Gaggawa Na Kawar Da Polio Ta Kasai ta ma tana da shaidar cewa lallai akwai wasu jami’an gudanar da rigakafi da ake bukatar saukewa daga kan wannan aikin.
Jihar Kano tana daya daga cikin jihohin da har yanzu ake samun bullar cutar shan Inna ta Polio, koda yake yau shekara daya ke nan ba a samun rahton bullar wani jinsin kwayar cutar Polio da ake kira WPV a takaice ba.
Hukumar ta ce duk da wannan, Najeriya tana kan hanyarta ta kawar da cutar Polio, a bayan da ta samu nasarar takaita yaduwar kwayar cutar.
Darektan hukumar kiwon lafiya matakin farko ta Najeriya, Dr. Ado Mohammed, yace a yanzu an takaita inda cutar Polio take zuwa jihohin Borno, Yobe da Kano kawai.