Da yake magana a wurin wani taron da Muryar Amurka ta shirya kan yaki da Polio a Kano, Malam Tudunwada yace tilas ne a samu hadin kan bangarori guda biyar idan ana son cimma gurin kawar da wannan cuta kamar yadda aka yi a akasarin kasashen duniya in ban da Najeriya da Afghhanistan da Pakistan da suka rage kawai a yanzu.
Wadannan sassan in ji shi sune Likitoci, malamai, sarakuna, ma’aikatan tsabta da kuma su kansu masu fama da wannan cuta ta Polio. Yace irin lafazi da kuma misalin da magidanci zai gani a jikin mai fama da cutar shan inna, yana iya canja masa ra’ayi ya kyale a ba dansa ko diyarsa maganin.
Haka kuma yayi suka da kakkausar harshe kan yadda mutane suke tare ruwan saman da ya kwararo a gefen titi wai sun a wanke Babura, yana mai fadin cewa tana yiwuwa a yada cutar Polio ta wannan hanyar idan ruwan ya kwaso kazantar bayangidan mai fama da wannan cuta.
Yayi kiran da a dauki mataki mai karfi kan wannan mummunar dabi’a.