Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Za Ta Fitar Da Dokar Shan Taba


Shan Taba Sigari a Najeriya
Shan Taba Sigari a Najeriya

Najeriya ta sake yin yunkurin kafa dokar da ta shafi shan taba, wani yunkuri da cikin shekaru masu zuwa zai iya ceton rayukan milyoyin matasan Najeriya daga cututtuka da kuma mutuwar dake da dangantaka da shan taba.

Najeriya ta sake yin yunkurin kafa dokar da ta shafi shan taba, wani yunkuri da cikin shekaru masu zuwa zai iya ceton rayukan milyoyin matasan Najeriya daga cututtuka da kuma mutuwar dake da dangantaka da shan taba.

Wannan dokar da yanzu take jiran amincewar yan majalisa, ta kushi abubuwa da dama kamar su kayyade wuraren da mutum zai iya shan taba, gargadi game da dangantakar da shan taba yake da shi ga lafiya, da kafa dokar da zata shafi talla da kuma tallafawa taba.

Sai dai kuma ta wurin wani karkataccen kampe da suka yi ta gudanarwa ta kafofin watsa labaru cikin yan watannin da suka wuce, wani kamfanin taba na duniya dake da babban rabo a kamfanin saida taba na Najeriya – yana kokarin hana fitar da wannan dokar.

Ta wurin kokarin samun tagomashi daga masu yin doka da kuma sauran mutane ta wurin yin amfani da wata takarda wadda babu gaskiya cikinta, kamfanin yana kokarin jawo hankalin al’umma don gurgunta wannan doka da zata ceto rayuka – kamar yadda tayi a shekara ta 2009 ta wurin wani gaggarumin kampe wanda ya hana wannan doka wucewa.

Har yanzu kasar Najeriya na da damar tsayawa gaba da taba domin ta tabbatar da kokarin wannan kamfani bai lalatar da lafiyar al’ummar ta ba. Lokaci yayi da ‘yan majalisar Najeriya zasu sake duban abin da yafi muhimmanci a garesu. Shin suna so su hada kansu da kamfanin da yake yiwa jama’arsu karya kuma yake sayas da abinda ke kashe jama’a? idan ‘yan majalisar kasa sun tabbata cewa sun mika kansu domin ceton rayuka da kuma kare hakin jama’arsu, ba kin hada kai da kamfanonin taba kadai zasu yi ba, amma dole ne su tashi tsaye su tabbatar wannan dokar ta yaki da taba ta zauna da gindinta.

Kamfanonin taba suna iza wata wuta ta bala’i a duniya – wanda ke kawo mutuwar kusan mutane miliyan shida kowacce shekara. Ba inda wannan yafi muni kamar a kasashen Afrika, wadda, kamar yadda kungiyar kansa ta Amurka ta fada, zata zama cibiyar cututtuka dake da dangantaka da shan taba a duniyar.

Yayinda kamfanin taba ke kokari sosai domin sayar da kayansa a wannan sashi, idan ba’a tashi tsaye ba, binciken ya nuna cewa yawan masu shan taba zai tashi daga mutane milyan 77 da ake da su a yau zuwa kimanin milyan 572 a shekara ta 2100.

Maganin wannan a fili yake. Idan aka fitar da ita, dokar hana shan taba ta kasa zata kare miliyoyin matasa ‘yan Najeriya daga rayuwa mara ma’ana. Wannan dokar na dauke da hanyoyin kiyaye ‘yan Najeriya kamar sauran kasashe na duniya dake karkashin kokarin kungiyar lafiya ta duniya akan kiyaye shan taba, wanda ake kira da suna dokar duniya ta hana shan taba, wadda ke da ikon ceton miliyan 200 na rayukan wadanda suka aiwatar da wannan.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG