Jami'in Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, Dr. Nuhu Barau Ningi, yace sun gudanar da bincike suka gano cewar a zagayen baya na rigakafin Polio da aka yi, an tsallake kimanin kashi 10 cikin 100 na yaran da ya kamata a ba su wannan maganin. Don haka ne yace tilas a gudanar da wannan sabon gangami na musamman da nufin tabbatar da cewa ba a ba wannan kwayar cuta sukunin yaduwa ko bulla ba.
Shugaban majalisar karamar hukumar ta Darazo, Alhaji Kabiru Adamu Sade, ya bukaci jama'a da su bayarda hadin kai domin tabbatar da an ja burki ma wannan cuta.
Wakiliyar Muryar Amurka, Amina Abdullahi Girbo, ta aiko da karin bayani daga Bauchi...