EU ta janye jakadan na ta ne domin ta ji ta bakinsa bayan da gwamnatin Nijar ta zarge shi da saba ka'ida da saka son rai wajen kasafta wani tallafin jin kai na Euro milion 1.3 da kungiyar ta bayar domin agaza wa 'yan Nijar da ambaliyar ruwa ta shafa.
A baya-bayan nan, an samu rikici tsakanin magoya bayan jam'iyyar NPP mai mulki da kuma babbar jam’iyyar adawa ta NDC, a unguwar Maamobi dake birnin Accra da kuma garin Ejura dake yankin Ashanti, wanda ya kawo damuwa ga shugabancin al’ummar Zango.
Shugabannin kungiyoyin kwadago da na jam’iyyun siyasa da jami’an fafutika masu yaki da akidar mulkin mallaka daga kasashen Afrika, Asia da na kudancin Amurka ne ke halartar wannan taro.
Tuni aka maye gurbinsa da tsohon ministan ci gaban karkara Kanal Abdoulaye Maiga.
A wani abinda ke fayyace alamun baraka a tsakanin hukumomin Mali, fira ministan gwamnatin rikon kwaryar kasar, Dr Choguel Maiga ya caccaki shugaban rikon kwaryar kasar, Janar Assimi Goita da mukarrabansa.
An yi garkuwa da wani fitaccen 'dan siyasar Uganda Kizza Besigye, bangaren adawa yayin bikin kaddamar da littafi a kasar Kenya a karshen makon daya gabata
Malaman makaranta a Jamhuriyar Nijar sun fara yajin aikin kwana biyu daga yau Litinin da nufin tada hukumomi daga barci a game da wasu dadaddun bukatun da suka ce an yi biris da su duk kuwa da cewa magana ce ta kyautata rayuwar malamai
Hukumomi a Gabon sun ce masu kada kuri’a sun amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar, fiye da shekara guda bayan da sojoji suka hambarar da Shugaban kasar da ya dade yana mulki, suka kwace mulki a kasar da ke tsakiyar Afirka mai arzikin man fetur.
Shugaban kasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya bukaci kasashen duniya da su dauki kwararan matakai don dakile tasirin sauyin yanayi da kuma kare makomar al'ummomi masu zuwa.
Kungiyar Transparency International ta gargadi mahukuntan Jamhuriyar Nijar da su soke yarjejeniyar ayyukan gina matatar da suka cimma da kamfanin Zimar na kasar Canada bayan da ta ce bincikenta ya gano cewa kamfanin Zimar na daga cikin irin kamfanonin da ke kewaye wa hanyoyin biyan haraji
A yau Talata, kasar Chadi ta bayyana amincewa da baiwa kamfanin samar da sadarwar intanet ta hanyar amfani da tauraron dan adam “Starlink”, mallakin attajiri Elon Musk, izinin sada kasar dake yankin tsakiyar Afrika da na’urar da nufin inganta sadarwar intanet
Shugabanin kabilun karkarar Filingue dake jihar Tilabery a Nijar sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya a yayin taron sulhun da hukumar wanzar da zaman lafiya ta shirya da nufin kawo karshen zaman doya da manja da aka fuskanta tsakanin al’umomin yanki mai fama da aika-aikar ‘yan bindiga da barayi.
Domin Kari
No media source currently available
Sojojin haya na kungiyar Wagner suna ci gaba da gudanar da ayyukansu duk da mutuwar shugabansu Yevgeny Prigozhin a watan Agustan 2023
Bayan kammala zaben shugaban kasa a Ghana, manazarta na ci gaba da yin tsokaci kan yadda aka gudanar da zaben
Wasu ‘yan uwa biyu daga Kenya suna ba da gudunmowarsu wajen kare muhalli inda suke amfani da takardun jarida wajen yin fensuran rubutu.
Zababben Shugaban Amurka Dobald Trump ya wallafa wasu sakonni a kafafen sada zumunta na barazanar kara haraji kan Canada, China da Mexico
A jihar Kano dake Najeriya ana zargin wani da cin zarafin wata ma'aikaciyar jinya mai dauke da juna biyu a asibitin yara ta Isyaka Rabiu
A Nijar an bude wata kasuwar baje koli ta ayyukan hannu da ake kira SAFEM, da matan kasar ke halarta daga jihohin da wasu kasashen Afirca