Masu fashin kan sha'anin tsaro sun ce matsalar hare-haren na da alaka da tsamin dangantaka da aka samu tsakanin Nijar da Faransa bayan juyin mulkin da aka yi.
Wannan sabuwar dambarwa ta kunno kai ne kwana guda bayan da wata tawagar manyan malaman addinin Islama daga Najeriya ta kai ziyarar shiga tsakani a rikicin siyasar kasar.
Wata tawagar malaman addinin Islama ta ziyara a birnin Yamai a ranar Assabar inda suka gana da shugabannin mulkin sojin jamhuriyar Nijar da suka hada da Janar Abdourahamane Tchiani da Firai Minista Ali Mahaman Lamine Zeine.
Wasu 'yan Nijar na ganin Faransa ba ta tabuka wani abin a-zo-a-gani a yakin da take yi da ayyukan ta'addanci a kasar da ma yankin Sahel baki daya.
Sabuwar gwamnatin ta rikon kwarya wacce Firai Minista, kuma Ministan kudin kasa Ali Mahaman Lamine Zeine zai jagoranta na da mambobin 21
Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun zargi kasar Faransa ta kai hari kan wasu askarawan kasar da sanyin safiyar yau Laraba 9 ga watan Agusta a wani kauyen Jihar Tilabery, abin da ya haddasa asarar rayuka, koda yake kawo yanzu ba a tantance adadinsu ba.
Sojojin da suka yi juyin mulki a jamhuriyar Nijer sun nada Ali Mahaman Lamine Zeine a matsayin Firai Ministan Gwamnatin rikon kwaryar da suke shirin kafawa a dai dai lokacin da karamar sakatariyar Amurka mai kula da harakokin siyasa Victoria Nuland ta kai ziyara a Nijar.
Wata hira ta musamman da wani mai sharhi a kan al'amuran yau da kullum a Nijar game da rashin Zartas da kudurin CEDEAO.
A yayinda wa’adin da ECOWAS ta bayar don mayar da shugaban Nijar Mohamed Bazoum kan mukaminsa ya shude a jiya Lahadi, sojojin da suka yi juyin mulki sun kara tsaurara matakai da nufin tunkarar barazanar amfani da karfin sojan da kungiyar ECOWAS ta ayyana don korarsu daga fadar ta shugabancin Nijar.
Gwamnatin mulkin sojan ta Nijar, ta sallami wasu jakadun kasar da suka hada da na Amurka, Faransa, Najeriya da Togo.
Jam'iyyar PNDS Tarayya ce ta sanar da wannan matakin da sojojin suka dauka yayin da a daya gefen kuma hukumomin sojin ba su ce uffan ba kan lamarin.
Jagoran sojojin da suka yi juyin mulki ya yi wannan ikirarin ne a wani lokacin da ake jiran zuwan tawagar ECOWAS/CEDEAO karkashin jagorancin Janar Abdulsalami Abubakar domin samo bakin zaren wannan rikici cikin ruwan sanyi.
Manazarta sha’anin tsaro na ci gaba da bayyana matsayinsu dangane da barazanar amfani da karfi da kungiyar CEDEAO ta yi wa sojojin Nijer akan bukatar su mayar da hambararen shugaba Mohamed Bazoum kafin cikar wa’adin mako daya.
Haka kuma majalisar sojojin ta sanar da bude iyakokin kasar ta Nijar da wasu kasashen da ba su da alaka da ECOWAS.
A yayin da gwamnatin Faransa ta ayyana shirin kwashe ‘yan kasarta daga Nijar, kasashen Mali da Burkina Faso sun jaddada goyon baya ga sojojin da suka yi juyin mulki a kasar.
A jamhuriyar Nijar kungiyoyin rajin kare hakkin bil adama sun bukaci bangarorin da ke takaddama a rikicin siyasar da ya sarke a kasar da su rungumi hanyar sulhuntawa da juna.
Shugaban kasar Chadi ya isa birnin Yamai a yammacin ranar Lahadi jim kadan bayan kammala taron kungiyar kasashen ECOWAS.
Shugabanin kasashen kungiyar ECOWAS za su gudanar da taro a Abuja don tantauna inda zasu bullo wa sojojin da suka yi juyin mulki a jamhuriyar.
Jam’yar PNDS Tarayya madugar kawancen jam’iyun hambarariyar gwamnatin Nijar ta musanta zargin hannun tsohon Shugaban kasa Issouhou Mahamadou, a juyin mulkin da soja suka yi wa Mohamed Bazoum a ranar Larabar ta gabata.
Sojojin da suka kifar da shugaba Mohamed Bazoum a ranar Larabar da ta gabata a Jamhuriyar Nijar sun zabi kwamandan rundunar tsaron fadar Shugaban kasa General Abdourahamane Tchiani a matsayin shugaban majalissar CNSP domin ya jagoranci al’amuran kasar.
Domin Kari