Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NAKASA BA KASAWA BA: Nakasassu Sun Fara Koyon Ayyuka Da Sana’o'in Hannu Don Kare Mutunci Kansu, Kashi Na Biyu - Satumba 28, 2023


Souley Mummuni Barma
Souley Mummuni Barma

A makon jiya shirin ya maida tabo halin da masu bukata ta musamman ke ciki a Burkina Faso da irin gudunmowar da suke bayarwa a harakokin ci gaban al’ummar wannan kasa.

A kashi na farko na tantaunawar wakilin sashen Hamza Adams da Usman Mohammed mai kere kere kayayakin fata a Ouagadougou an ji yadda ya koyi wannan sana’a dake matsayin madogarar rayuwa a gareshi .

Sanin kaskancin da ke tattare da bara ya sa Malan Usman ware lokaci domin jan hankulan nakasassun da mutuwar zuciya da rashin samun kulawa daga al’umma suka jefa cikin wannan haraka.

To kashi na biyu kuma na karshen wannan tantaunawa zai maida hankali kan yanayin mu’amula a tsakanin masu bukata ta musamman da yadda abin yake a tsakaninsu da al’umma da kuma mahukuntan Burkina Faso.

Saurari shirin:

NAKASA BA KASAWA BA
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:59 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG