Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Issouhou Mahamadou Na Fuskantar Barazanar Gurfana Gaban Kotun ICC


Shugaba Issouhou Mahamadou
Shugaba Issouhou Mahamadou

Kungiyar M62 ta gabatar da takarda a ofishin ministan harkokin wajen Nijar akan bukatar maka tsohon Shugaba Issouhou Mahamadou a kotun kasa da kasa ta ICC, saboda zarginsa da aikata miyagun laifuka da zama silar aika-aikar ‘yan ta’addan da ake fama da su, abinda makusantansa ke cewa zancen banza ne.

Rashin gudanar da mulki nagari a zamanin da ya shugabanci kasa na daga cikin abubuwan da kungiyar M62 ke dauka a matsayin hujjojin da ta ce ta jinginu da su wajen bijiro da wannan magana ta shigar da karar Shugaba Issouhou Mahamadou a kotun ICC ko CPI, saboda yadda abin ya jefa al’umma cikin halin kuncin rayuwa kamar yadda wata jigo a kungiyar ta M62 Falmata Taya ta bayyana.

Yaduwar ayyukan Boko Haram daga Najeriya zuwa Nijar, da bazuwar rikicin arewacin Mali zuwa Nijar abubuwa ne da M62 ke dora alhakin faruwarsu a wuyan tsohon Shugaban kasa Issouhou Mahamadou, a saboda haka kungiyar ta shiga yunkurin ganin kotun hukunta manyan laifuka ta gurfanar da shi.

To sai dai wani na hannun daman Shugaba Issouhou wato Alhaji Assoumana Mahamadou, ya yi watsi da wadannan zarge-zarge, ya na mai bayyana matakin kungiyar tamkar wani yunkurin zubar da kimar kasa a idon duniya.

Takardar karar wacce shugabanin M62 suka damka a hannun ma’aikatar harkokin wajen Nijar a yammacin Talata 3 ga watan Oktoba na dauke da bukatar ganin kotun ICC ta bi diddigin zargin Shugaba Issouhou da zama mafarin shigowar ayyukan ta’addanci a kasar.

Haka kuma kungiyar ke fatan ganin an hukunta dukkan wani jami’in ciki ko na wajen wannan kasa da dukkan wata kasa da aka tabbatar da samun hannunta a ta’asar da ‘yan ta’adda ke haddasawa.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Issouhou Mahamadou Na Fuskantar Barazanar Gurfana Gaban Kotun ICC
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG