Tsohon shugaban Nijar Mahamadou Issouhou ya bayyana fatan ganin shugabannin kasashen ECOWAS/CEDEAO sun jingine dukkan wani shirin amfani da karfin soja wajen warware wannan matsala.
Kiran Issouhou na zuwa ne yayin da ake cika watanni biyu da barkewar rikicin siyasar da ya biyo bayan juyin mulkin da soja suka yi wa shugaba Mohamed Bazoum.
A cewar tsohon shugaban kasar, tattaunawa cikin ruwan sanyi ita kadai ce hanyar da za ta ba da damar samar da mafitar wannan dambarwa.
Ta hanyar wani sakon da ya kafa a shafinsa na X, tsohon shugaban kasa Issouhou ya fara da bayyana abin da ya kira damuwarsa game da babban rikicin da Nijer ta tsinci kanta.
A dalilin haka, ya jaddada cewa tattaunawa ce kadai za ta ba da damar bude hanyar gaggauta maido da cikakkiyar dimokradiya.
Shugaban kungiyar RODHADD mai kula da kare hakkin dan adam Laouan Salao Tsayabou TSA ya yaba da matsayin na tsohon shugaban kasa.
Tsohon dan majalissar dokokin kasa na jam’iyar PNDS Tarayya Abdoul Moumouni Gousmane na daga cikin masu jinjina masa saboda wannan yunkuri na neman kashe wutar rikici a cewarsa.
Wannan shi ne karo na biyu da tsohon shugaban Nijar ke bayyana matsayinsa a game da abubuwan da ke wakana a kasar bayan da soja suka ba da sanarwar juyin mulki.
A sakon farko da ya kafa a shafinsa na X a ranar 30 ga watan Yuli ya sanar cewa ya shiga yunkurin samar da hanyoyin warware kullin da ya sarke cikin ruwan sanyi ta yadda za a saki shugaba Mohamed Bazoum a kuma mayar da shi kan kujerarsa.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna