Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Awon Gaba Da ‘Yar Jarida A Nijar Har Yanzu Babu Duriyarta


Samira Sabou, ‘yar jarida kuma shugabar kungiyar masu fafutika ta yanar gizo a Nijar
Samira Sabou, ‘yar jarida kuma shugabar kungiyar masu fafutika ta yanar gizo a Nijar

Kungiyoyin kare hakkin ‘yan jarida a Jamhuriyar Nijar sun bayyana damuwa bayan da wata ‘yar jarida kuma shugabar kungiyar masu fafutika ta yanar gizo Samira Sabou ta yi batan dabo a yammacin ranar Asabar din da ta gabata.

NIAMEY, NIGER - Lamarin da ke zama tamkar wata manuniya game da hadarin da ke tattare da aikin jarida tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar a ranar 26 ga watan Yuli.

Labarin bacewar Samira Sabou ya fara bayyana ne a karshen mako a kafafen sada zumunta inda aka sanar cewa ba a san inda ‘yar jaridar ta shiga ba, lamarin da wasu suka fara hasashen yiwuwar abu ne da ba zai rasa nasaba da wasu labaran da ta wallafa a shafinta na Facebook ba a makon da ya shige.

Hakan ya sa aka tuntubi mataimakinta a kungiyar ABCA da take jagoranta, Mamoudou Djibo Hamani wanda ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce tabbas an yi awon gaba da Madame Samira Sabou tun ranar Asabar 30 ga watan Satumba a wajejen karfe 5 da minti 30 na yamma.

Ya ce wasu mutane ne sanye da kayan farar hula suka tafi har gidanta suka dauke ta, kuma tun daga wancan lokaci ba a sake jin duriyarta ba. Ya ce sun kuma tafi ofishin ‘yan sandan farin kaya amma an sanar da shi cewa Samira ba ta wurin.

Saboda haka suna ci gaba da nemanta amma har yanzu ba su samu wasu bayanan da ke nunin inda ta ke ba. Ya ce “muna cikin damuwa sosai a game da halin da take ciki. Muna kira a gaggauta sakinta ba tare da wani sharadi ba.”

Kungiyoyin ‘yan jarida sun dukufa da bin diddigin wannan al’amari da nufin gano inda aka shiga da madame Samira Sabou inji shugaban cibiyar ‘yan jarida ta kasa Maison de la Presse, Ibrahim Harouna.

Kawo yanzu hukumomi ba su yi bayani kan wannan al’amari ba ballantana a iya sanin ko Samira na hannunsu ko kuma hannun wasu masu aika-aika ta shiga a bisa la’akari da yadda ta koka a baya cewa wasu na yi ma ta barazana ta wayar talaho saboda abubuwan da take yadawa a yanar gizo.

Majalissar CNSP a sanarwar farko da ta fitar bayan juyin mulkin 26 ga watan Yuli ta jaddada aniyar mutunta dukkan yarjeniyoyin kasa da kasa da Nijar ta saka wa hannu ciki har da batun kare hakin ‘dan adam da mutunta aikin watsa labarai.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

 An Yi Awon Gaba Da Wata ‘Yar Jarida A Nijar Sakamakon Wasu Furcenta .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG