Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Ya’yan Jam'iyyar PNDS Sun Zargi Issouhou Mahamadou Da Hannu A Juyin Mulkin Da Aka Yi A Nijar


Shugaba Issouhou Mahamadou
Shugaba Issouhou Mahamadou

Cece-kuce ya barke bayan da wasu 'yan jam’iyyar PNDS na kusa da tsohon shugaba Issouhou Mahamadu suka fara zagaya jihohin Nijar don tsara gangamin goyon bayan gwamnatin sojan kasar, lamarin da magoya bayan Bazoum ke kallo a matsayin wanda ke gaskanta zargin hannun Issouhou a juyin mulkin watan Yuli.

Ta hanyar wata takardar sanarwar da aka wallafa a kafafen sada zumunta da wasu tarin muryoyi da suka karade irin wadanan kafafen ne aka sami labarin jam’iyyar PNDS Tarayya da wasu kawayenta na shirye-shiryen gudanar da taron gangami a wannan makon a birnin Tahoua da nufin goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulki, matakin da makusantan hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum ke dauka tamkar wata kwakkwarar hujja da ke gaskanta zargin hannun tsohon shugaba Issouhou Mohamadou a abubuwan da suka wakana a ranar 26 ga watan Yuli.

Sahanine Mahamadou, daya daga cikin masu bai wa hambararren shugaban shawara, ya fadi cewa Issouhou Mohammadou ya tura kudi miliyan hamsin don a shirya taron gangamin a jihohi, abin da ke tabbatar da cewa Issouhou shi ya yi juyin mulki, a saboda haka ‘yan Nijar su yi hattara a cewarsa.

To sai dai a na su bangaren magoya bayan Shugaba Issoufou na cewa babu kowace irin alaka da harakokin siyasa a taron da suke shirin gudanarwa, haka kuma suna kalubalantar masu zargin tsohon shugaban da hannu a wannan juyin mulki kamar yadda wani hadimin tsohon shugaban Assoumana Mahamadou ya bayyana.

“Mutane na da mantuwa, a lokacin da Issouhou ya nuna goyon baya ga Bazoum babu irin zagin da ba a yi mushi ba, amma yanzu don ya ce bai so a kai wa Nijar hari sai a ce bai son Bazoum?” a cewar Assoumana.

Majalissar CNSP, a washegarin juyin mulkin na ranar 26 ga watan Yuli ta bada sanarwar dakatar da ayyukan jam’iyyun siyasa a dukkan fadin Nijar, sabili kenan shugaban kungiyar Voix Des sans Voix Nassirou Saidou ke jan hankalin hukumomi da ‘yan siyasa kan bukatar mutunta wannan mataki.

Wannan dambarwa ta tsare-tsaren gangamin goyon bayan jam’iyyun siyasa da kace-nacen da ya kunno kai a tsakanin magoya bayan PNDS Tarayya na faruwa ne a wani lokaci da alamomin radadin takunkumin kungiyar CEDEAO suka fara bayyana a harkokin jama’a na yau da kullum, kamar hauhawar farashin ababen masarufi da kuma dauke wutar lantaki a kai a kai duk da matakan cikin gida da gwamnatin mulkin sojan ke dauka da zummar tunkarar lamarin.

Saurari rahoton Souley Moumouni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG