WASHINGTON DC —
A wannan mako shirin zai maida hankali kan halin da ilimin nakasassu ke ciki a Jamhuriyar Nijar inda a farkon watan nan na Oktoba aka bude makarantun Framary da sakandare bayan kammala babban hutu.
Makarantar makafi Ecole Soly Abdourahamane da ke birnin Yamai na daga cikin makarantun da ake alfahari da su a kasar Nijar akan maganar ilimantar da yara masu bukata ta musamman.
Sai dai karancin kayayyakin gudanarwa ya haddasa cikas a bana wajen bude wannan makaranta lokaci guda da daukacin makarantun bokon kasar kamar yadda za a ji Karin bayani daga daya daga cikin shugabaninta Malan Moussa Nasser.
Saurari shirin:
Dandalin Mu Tattauna