Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da masu ruwa da tsaki kan harkar tsaron kasar.
Wakilan kwamitin sulhu sun tashi zuwa Afirka ta yamma domin ganewa kansu matsalolin tsaro da kasashe dake raya tafkin Chadi da kuma mummunar yanayin zamantkewa da suke fuskanata a yankin.
Rundunar sojan Najeriya na Operation Lafiya Dole dake garin Maiduguri, tace ta samu nasarar kubutar da wasu mutane 7,896 daga hannun ‘yan kungiyar Boko Haram.
Hukumar yaki da fataucin mutane ta Najeriya ta kaddamar da bincike kan wasu mata yara kanana da aka yi fataucinsu zuwa kasar Mali, domin yin harkar karuwanci.
Ma’aikatar lafiya ta jihar Borno ta tabbatar da cewa an gano wata mata ‘dauke da ciwon zazzabin Lassa, wanda yayi sanadiyar rayuka a wasu yankuna a Najeriya.
Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da jawabinsa na farko a gaban ‘yan Majalisun tarayya, bayan da aka rantsar da gwamnatinsa a watan da ya gabata.
Jiya Talata da Rasha da China sun hau kujerar na ki don taka burki ma wani yinkuri a Kwamitin Sulhun MDD na kakaba ma gwamnatin Siriya takunkumi saboda amfani da makamin guba kan jama'arta.
Jama’ar jahar Unity, ta kasar Sudan ta Kudu, daya daga cikin yankin da ya fuskanci matsanancin fari, sun ce sun rayu ne ta amfani da cin ‘ya’yan itace da kuma tsiron dake fitowa kan ruwa har na tsawon shekaru 3.
Mutumin da shugaba Donald Trump ya zaba ya zama shugaban hukumar leken asirin tsaron kasa ya bayyana Rasha a matsayin babbar barazana ga Amurka.
Shugaban jam’iyyar PDP Sanata Ali Modu Sheriff ya shiga ofis a hedikwatar jam’iyyar ta Wadata Plaza dake Abuja.
Jiya Talata wani babban jami’in kungiyar kawancen NATO, ya yi kira ga hukumomin yankin Abkhazia da Rasha ta mamaye, wanda wani bangaren kasar Georgia ne, da su sake tunani game da shirinsu na rufe wurare biyu na shiga yankin da ke karkashin ikon gwamnatin Georgia mai fada a Tbilisi.
Yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’ar samun lafiya, tsohon shugaban kasar Janar Yakubu Gowon, ya nuna damuwarsa game da yadda ake saka siyasa a rashin lafiyar shugaban ‘kasa.
Noma Tushen Arziki
Sojojin Iraqi da ke yaki da ISIS sun isa wata muhimmiyar gada a cikin birnin Mosul, yayin da su ka kara dannawa a himmar da su ka fara tun mako guda da ya gabata ta fatattakar ISIS daga sashin yamma na birnin.
Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe, ya yi bukin zagayowar ranar haihuwarsa karo na 93, tare da kawar da duk wani tsammanin cewa zai yi murabus ko kuma ba zai sake tsayawa takara ba.
Wata kotun tarayyar Najeriya ta yankewa wata mata hukuncin ‘dauri bayan da aka same ta da laifin yunkurin safarar hodar iblis daga Najeriya zuwa Saudiya.
Rundunar ‘yan Sandan Najeriya ta samu nasarar kama mutane 104 a cikin wannan watan, da ake zargin su da hannu a wasu laifuka da suka hada da kisan kai a jahar Neja.
A bana ma kamar sauran shekaru tun fara gasar tsere kan tsaunin kamaru mai tsawon mita dubu hudu, 'yan kasar mace da na miji ne suka suka zo na daya.
Shugaban Amurka Donald Trump yace yana jin za'a kara yau Litinin kan batun rusa dokar kiwon lafiya da ake fi sani da Obamacare da maye gurbinta, a lokacin da zai gana da gwamnonin Amurka anan birnin Washington.
Jam’iyyar PDP mai mulki ta lashe zaben dukkannin yankunan kananan hukumomin jahar Gombe.
Domin Kari