"Idan na ga cewa ba zan iya cigaba ba, zan gaya ma jam'iyya ta saboda a saukaka ma ni," abin da ya gaya ma kafar labaran gwamnati ta ZBC-TV kenan. "To amma zuwa yanzu ina ganin, ba zan iya cewa haka ba. Yawancin mutane na ganin a hakikanin gaskiya babu madadi na. A garesu babu wani magajin da zai samu karbuwa, musamman karbuwa irin tawa."
Kalami na karshen na iya zama gaskiya, ganin cewa babu wani fitaccen jagoran 'yan adawa a Zimbabwe a yanzu. To amma shekarun Shugaban na nuna cewa ko ba dade ko ba jima, dole ne mutanen Zimbabwe su nemi wani sabon Shugaban kasa, kuma tuni ma fafatawar gadarsa ta zafafa a jam'iyyar ZANU-GF mai mulki.
Akwai bangarori biyu da su ka fito baro-baro su na gwagwarmaya kan mukamin na Shugaban kasa, wato da Generation 40 (ko G40) da kuma Team Lacosta. Generation 40, wanda ke nufin matasan da ke cikin jam'iyyar, na da alaka da matar Shugaban kasar, Grace Mugabe, a yayin da kuma Team Lacoste ke goyon bayan Mataimakin Shugaban Kasa Emmerson Mnangagwa.
Facebook Forum