Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta da hadin gwiwar jami’an leken asiri na DSS sun cafke wasu ‘yan Boko Haram ‘yan kasar Chadi a jihar Gombe.
Kungiyar matasa Kristoci masu wanzar da salama da kuma reshen matasa na kungiyar Kristocin Najeriya CAN sun gudanar da taron wanzar da zaman lafiya a birnin Abuja.
An gudanar da taron daurin auren zawarawa da ‘yan mata su fiye da 1500 a fadin kanan hukumomin jahar Kano 44.
Babban kwamandan sojojin Amurka dake Afirka ya fada wa Muryar Amurka cewa, hanyar kawai da za a iya samar da zaman lafiya a kasar Libya itace ta hado bangarorin dake fada da juna wuri guda.
An samu gawarwakin ‘yan gudun hijira har su 13 cikin kwantenar jirgin ruwa lokacin da ake kokarin tsallakawa da ita a kudancin kasar Libya.
Mahukunta a kasar Gambia sun bada labarin cewan gwamnatin kasar ta kame tsohon shugaban hukumar tattara bayanan sirri na kasar, wanda ake zargi da aikata laifin take hakkin bil adama a zamanin tsohuwar gwamnatin data shude ta Yaya Jameh.
Gwamnatin Najeriya ta ce za ta bi kadun `yan kasar da aka jikkata tare da kona musu dukiya a kasar Afirka ta kudu, biyo bayan rikicin kyamar baki.
Rundunar Sojojin Najeriya da masu fafutukar kare hakkin bil Adama sun mayar da martani bisa rahotan da Amnesty International ta fitar.
Tsohon shugaban Amurka Barack Obama, ya shawarwaci magajinsa kafin ya sauka cewa ya nemi karin goyon bayan China, wajen shawo kan Koriya ta arewa game da shirin Nukiliyar kasar, kamar yadda wani tsohon jami'i a gwamnatin Obama- Jon Wolfsthal, wanda yake da masaniya game da batun ya fada.
An yi kira ga ‘yan Najeriya su yi wa shugaban kasa Mohammadu Buhari da kasar baki daya addu’a maimakon zage-zagen batanci.
Jiya Laraba, sabon shugaban Somalia Mohammed Abdullahi Mohammed, wanda aka fi sani da inkiyar "Farmajo" yayi rantsuwar kama aiki, a bikin ne shugaban yayi alkawarin daidaita al'amura a kasar da yaki ya daidaita, amma yayi gargadin cewa, aikin zai dauki shekaru masu yawa.
Shugaban Amurka Donald Trump, yayi watsi da zanga-zangar da ta barke kan yunkurinsa na wargaza inshoran kiwon lafiya wadda ya kasance daya daga cikin nasarorin da shugaba Obama ya samu zamanin mulkinsa.
Wata tawagar wakilan majalisar dokokin Amurka data dawo daga ziyara data kai Cuba, tace shugaban kasar Raul Castro, ya nuna sha'war ci gaba aiki domin inganta dangantakada Amurka, duk da alwashin da shugaban Amurka Donald Trump yayi na canza alkiblar danganataka tsakanin kasashen biyu.
Kusushoshi biyu a Majalisar ministocin shugaban Amurka Donald Trump, suna Mexico da zummar kwantar da hankali kasar game da damuwa da kuma fushinta kan sabbin manufofin Amurka kan kasar.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Antonio Gutierrez, jiya Laraba yayi gargadin cewa mutane milyan 20 a kasashe hudu suna fuskantar fuskantar 'yunwa idan ba hukumomin kasa da kasa sun dauki matakai na hana hakan aukuwa ba.
Wani rahoto da jaridar Guardian ta wallafa ya nuna wakilinta ya yi kundunbalar sanin halin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke ciki a gidan da yake a London, wanda ya sa ‘yan sanda suka yi awon da gaba da ‘dan jaridar.
Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello, ya fara rangadin kananan hukumomin jihar guda 25 da nufin samar da ababen more rayuwar mutanen karkara.
A jihar Gombe wani mai mata biyu ya rasa amaryarsa da kuma ‘ya ‘yansa guda shida a sanadiyar gobara da ta faru cikin dare.
Noma Tushen Arziki
Shirin daukar malamai 3000 aiki na tsawon wa’adin shekaru biyu ana biyansu albashin Naira 30,000 ga masu digiri, da kuma Naira 20,000 ga masu NCE da gwamnatin jihar Taraba ta kuduri aniyar yi ya gamu da shakku, ganin cewa tana fuskantar matsalar biyan albashi a jihar.
Domin Kari