Kwamandan rundunar major janar Lucky Irabor, shine ya bayyana hakan a wata hira da yayi da manema labarai a garin Maiduguri, yace cikin mutanen akwai kuma wasu mutane ‘yan kasashen waje guda takwas, wanda kuma suka hada da maza 914 da mata 2,388 da kuma kananan yara fiye da dubu biyu.
Baki daya mutanen an samu kubutar da su ne a wurare daban-daban a sakamakon ci gaba da kakkabe sauran ‘yan kungiyar Boko Haram din da ake.
Kwamandan yace ranar 1 ga watan Fabarairun wannan shekara sun sami nasarar kashe wasu ‘yan Boko Haram guda shida, a wata arangama da suka kai musu a kauyen Dasula dake karamar hukumar Dambua. Haka kuma a ranar 7 ga watan Fabarairun kuma sun kashe wasu ‘yan Boko Haram din guda 13.
Haka kuma rundunar ta kama tabar wiwi mai yawan gaske a wajen wani mutum da ya bayyana kansa a wajen wani dake bayyana kansa a matsayin ‘dan sanda wanda ke dauke da katin shaidar zama ‘dan sanda na jabu, a yankin Son dake iyaka da jahar Borno.
Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.
Facebook Forum