Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Zai Gana Da Gwamnonin Amurka


Shugaban Amurka Donald Trump yace yana jin za'a kara yau Litinin kan batun rusa dokar kiwon lafiya da ake fi sani da Obamacare da maye gurbinta, a lokacin da zai gana da gwamnonin Amurka anan birnin Washington.

Fiye da gwamnoni 40 ne suke nan Washington domin taron shekara shekara na kungiyoyin gwamnonin kasar.

Shugaba Trump ya karrama gwamnonin a wata liyafa da aka shirya musu a daren jiya Lahadi a fadar shugaban na Amurka ta White House yana cewa "manya manyan gwamnonin Amurka" koda kuwa wasu daga cikin gwamnonin basu amince da manufofin gwamnatinsa ba.

Dokokin shugaban na Amurka sun hada da matsin lamba kan bakin haure su akalla milyan 11, wanda ya hada da barazanar hana birane da suke baiwa bakin haure mafaka tallafin biliyoyin dala daga asusun tarayya.

Amma a hira da MA, wasu daga cikin gwamnonin sun ce suna son ganin bakin haure da 'yan gudun hijira da suka iso nan yanzu sun sami sukunin shirya rayuwa mai kyau anan Amurka. Haka nan sun jaddada muhimmancin mutunta kowa a yayinda ake aiwatar da dokokin.

Shugaban kungiyar gwamnonin, kuma Gwamnan Virginia, dan Democrat Terry McAuliffe, yace yana daukar sabbin dokokin shugaban kasan a zaman "maras imani ko tausayi kuma sun sabawa doka."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG