Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Fari a Wasu Yankunan Sudan Ta Kudu


Jama’ar jahar Unity, ta kasar Sudan ta Kudu, daya daga cikin yankin da ya fuskanci matsanancin fari, sun ce sun rayu ne ta amfani da cin ‘ya’yan itace da kuma tsiron dake fitowa kan ruwa har na tsawon shekaru 3.

Cibiyoyin aikin jin kai suka ce isa ga wadannan mutanen ya zame musu wani jan aiki har na tsawon watanni, yayin da ‘yan kauyen suka ce noma ya zame musu da whala domin yawan harbe-harben da sojoji keyi a yankin nasu.

Daya daga cikin shugabannin al’umma ya tattara dubban mutane, wadanda suka yi dogon layi domin yin rajistar samun tallafi daga hukumar samar da abinci da kuma UNICEF domin samun tallafi.

A cikin makon da ya gabata ne hukumomin MDD suka bayyana cewa fari ya addabi yankin gundumar Leer.

Wani dan shekaru 32 mai suna Ray Ngwen Chek, mai ‘ya’ya 8 yace fadan da ake yi tsakanin ‘yan tawaye da sojojin gwamnatin na daga cikin dalilan da su ka haifar da fari a wannan yankin nasu.

Ya ce wannan yakin shine ya lalata dukkan albarkatun gona a wannan yankin nasu, Yace idan an duba bawane irin shuka a wannan wurin, domin ko sun gaza shuka, don haka basu da abinci, yace ga yaran mu nan cikin rana suna kuka saboda da wannan farin, inji Chek.

Ya ce rayuwa a wannan wuri na cike da kalubale, domin sojojin gwamnati na nan nata fada da sojojin tsohon mataimakin shugaban kasa Riek Marchar.

Tun dai da yaki ya barke a kasar ta Sudan ta Kudu a cikin shekarar 2013 ‘yan kauye suka gudu suka bar gidajen su, wasu suka koma cikin daji da zama.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG