Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Daure Wata Mata Shekaru 10 Saboda Safarar Miyagun Kwayoyi


Hajiya Binuyo Basira Iyabo
Hajiya Binuyo Basira Iyabo

Wata kotun tarayyar Najeriya ta yankewa wata mata hukuncin ‘dauri bayan da aka same ta da laifin yunkurin safarar hodar iblis daga Najeriya zuwa Saudiya.

Alkalin babbar kotun tarayyar Najeriya, Justice Quadri, ya yanke hukuncin ‘daure Hajiya Binuyo Basira Iyabo wadda ta yi niyyar tafiya hajjin bara ta jirgin daular Larabawa Emirate daga filin saukar jiragen sama na Abuja, wacce ta hadiye hodar iblis mai nauyin gram 931.

Tun kama Hajiya Iyabo, wadda ta yi niyyar safarar hodar iblis din zuwa Madina, da jami’an hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi NDLE su ka yi, aka gurfanar da ita gaban kotu. Mai shari’a Quadri, ya yanke hukuncin ‘daurin shekaru 10 da aiki mai tsanani ga Iyabo, musamman ma duk tambayoyin da aka yi mata bata yarda ta fadi wadanda suka tura ta da hodar ba.

Kwamandan hukumar NDLE na filin saukar jiragen sama na Abuja, Hamisu Lawan, ya nuna farin cikin wannan hukuncin da ambatar wasu dabarun da dillalan kwaya ke yi. Yace hukumar NDLE na aiki tukuru wajen damke duk wasu masu cushen kwayoyi a kayayyakinsu domin sarafarsu zuwa kasashen waje.

Hukumar alhazan Najeriya ta bullo da bada lasisi ga kowacce jaha da hakan zai sanya ka’idoji na tantance maniyaci don gujewa take doka a Saudiyya, da kuma tabbatar da kare hakkokin alhazan bisa kudin da suka biya.

Masu sharhi na ganin Hajiya Iyabo ta tsalle rijiya da baya da aka gano ta tun a Najeriya, don Saudiyya kan yanke hukuncin kisa ne ga irin wannan laifin.

Domin karin bayani saurari rahoan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG