Jami'ai sun ce dakarun gwamnati na iko da wani sashin da ake kira Gada Ta Hudu, ko kuma gadar da ta ke kuryar kudu a tsallaken kogin Tigris. Yakin da ake yi a Mosul ya yi matukar lalatawa ko kuma rushe dukkannin gadoji kwata-kwata, amma sake samar da mahada bisa kogin zai ba da damar jigilar sojoji da kuma kayan aiki.
Yayin da yakin na yammacin Mosul ke kara tsananta, akwai damuwa kan makomar farar hulan da ke wurin. MDD ta bayyana cewa akwai matsalolin jinkai a yankin ta yadda jama'a ke fuskantar karancin abinci, da man fetur da kuma magunguna.
Da yawan farar hulan sun gudu ne zuwa yammacin Mosul bayan da aka tilasta masu barin gabashin birnin, wanda sojojin Iraki su ka kwato bayan fafatwa ta tsawon watanni uku da aka fara a watan Nuwamba.
Facebook Forum