Rufe wadannan wuraren ketarawa biyu da ke bakin iyakan yankin Abkazia dake kasar Georgia, wanda daruruwan ‘yan kasar ke anfani da su kullun, zai haifar da koma baya ga yanayin wanna yankin, dama cikas a wannan yankin, inji mai Magana da yawun NATO Oana Lungescu.
Ya ce muddin akayi haka to ba shakka hakan zai takaita yancin walwala kana ya kawo wa mazauna wannan wurin cikas, haka kuma Lungescu ya bukaci Rasha da kwana da sanin cewa tsohuwar tarayyar Soviet ta yarda da wannan bakin iyakar, kuma tana daukar kudancin Ossetia da Abkazia a matsayin yankin Georgia ne mai cin gashin kansu.
A cikin watan Disamban bara ne dai mahukuntan Rasha dake Abkazia suka bayyana cewa zasu rufe biyu daga cikin wuraren ketarawa hudu na kan iyakar wannan yankin, inda mafi yawan su ‘yan kabilar Gali ne na gundumar Georgia da kuma wadanda suke daura da Zugdidi daga kudanci.
Sashen muryar Georgio na wannan gidan radiyon ya ruwaito cewa muddin aka rufe wadannan bakin iyakokin, hakan zai takaita wa matasa har ma da dattawa yan kabilar Geogia daga samun damar zuwa makarantar gwamnati da kuma abubuwan dake da nasaba da kiwon lafiya.
Facebook Forum