Ma’aikata a jihar Adamawa na kokawa sakamakon zaftare musu albashi domin yin katin shaidar ma’aikata wato ID Card, batun da ma’aikatan suka ce ba zata sabu ba.
Gwamnatin jihar Taraba ta tanadi kayayyakin abinci a wani mataki na ragewa talakawanta radadin hauhawar farashi kayan, don rabawa ga dukkan mazabunta dake kananan hukumomi goma sha shida albarkacin watan azumi.
Shugaba Donald Trump na Amirka yace yau Alhamis din nan idan Allah ya yarda zai bada sanarwar shawarar daya yanke, akan ko ya fitar da Amirka daga yarjejeniyar tarihi da aka kula a Paris a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar akan yanayi ko kuma a’a.
Bam da aka boye cikin wata motar a kori kura ya fashe jiya Laraba da safe a unguwar da ofisoshin jakadanci suke a Kabul baban birnin kasar Afghanistan ya kashe akalla mutane casa’in da raunana fiye da mutane dari uku.
Hukumomin kasar Somaliya sunce wani kwamandan kungiyar yan tawayen Somaliya ta Al Shabab mai suna Bishar Mumin Farah, jiya Laraba yayi saranda ga sojojin gwamnatin kasar.
Shugabannin Fulani a yankin kudu maso yammacin Najeriya sun koka game da tafiyar hawainiya da gwamnati kasar ke yi wajen kawo karshen rikici tsakanin Manoma da Makiyaya.
A wani yunkuri na magance rashin aikin yi dake cikin manyan matsaloli da suka yi wa Najeriya dabaibayi,yanzu haka hukumomi a jihar Taraba sun horas da mata fiye da 200 domin dogaro da kai.
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargadin cewa sama da mutane Miliyan bakwai ne ke mutuwa a duk shekara sanadin matsalolin da suka danganci shan taba sigari, kuma tana kawo koma baya ga tattalin arzikin kasashe
A jiya Talata ne babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya bukaci gwamnatin Donald Trump da kada ta fice daga yarjejeniyar sauyin yanayin da aka cimma ta Paris, yana mai cewa yarjejeniyar na da muhimmanci ga tattalin arzikin Amurka da tsaronta.
A jiya Talata ne wata kotun soja a Sudan ta Kudu ta fara shari’ar wasu mutane 20 da aka zarga da laifukan kisa da fyade a wani hari da aka kai kan wasu masu aikin agaji na kasa da kasa a shekarar da ta gabata.
Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta rasa wasu ‘yan majalisun wakilai daga jihar Adamawa, batun da ya sake bude wata sabuwar dambarwa a jihar.
Bayan da hukumar alhazan Najeriya ta sanar da kudin zuwa aikin Hajjin mai zuwa da ke sama da Naira Miliyan Daya da rabi, al’ummar Musulmin kasar na ci gaba da kokawa akan karin farashin.
Matar tsohon gwarzon fafatukar neman yancin Sudan ta Kudu marigayi John Garang tana kira ga sojojin gwamnati su daina goyon bayan shugaba Salva Kiir.
A damokaradiyar Jamhuriyar Congo, har yanzu babu tabbas a kan lokacin da za a gudanar da zaben da ya kamata a gudanar bara. Sai dai An fara rajistar masu zabe a Kinshasa babban birin kasar.
Sabon shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya kira tashar watsa labarai ta RT da Kremlin ke marawa baya, a matsayin tashar farfaganda, bayan tattaunawarsa gaba da gaba da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin.
Shugaban Amurka Donald Trump ya karrama wadanda ya bayyana a matsayin sabbin jinin Amurkawa masu kishin kasa, wandada yace suna yaki da nufin murkushe ayyukan ta’addanci.
‘Kasa da mako uku bayan da wani gini mai hawa uku ya ruguje tare da kashe mutane uku, wani ginin mai hawa uku ya sake faduwa a Legas ya kuma kashe mutane biyu.
Gwamnatin jihar Filato ta nada kwamiti da zai gudanar da aikin gina babbar kasuwar Jos da aka fi sani da kasuwar Terminus, don habaka harkokin kasuwanci a jihar.
Koriya ta Arewa ta sake gwada wani makami mai linzami mai cin gajeren zango da safiyar yau Litini, yan kwanaki bayan da kungiyar kasashen masu arzikin masana’antu ta G-7 tayi kira ga Korea ta Arewa ta dakatar da shirinta na makaman nukiliya.
Domin Kari