Biyo bayan rugujewar ginin mutane biyu sun rasa rayukansu, haka kuma sami ceto wasu mutane 14 daga cikin baraguzan ginin. Rahotanni na cewa ginin ya ruguje ne a dai-dai lokacin da ake yiwa ginin kwaskwarima.
Jami’an hukumar bada agajin gaggawa na jihar Legas da jami’an ‘yan kwana-kwana da kuma ‘yan sanda ne suka saka ido wajen ceto mutanen da ke cikin ginin lokacin da ya rushe.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, ASP Olarinde Famous-Cole, shine ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai ya ce kawo yanzu basu da rahoto da ke tabbatar da dalilin rugujewar ginin. Amma a bangare guda kuma, Injiniyoyi da sauran masu harkar gine-gine a birnin Legas, na danganta rugujewar gidaje a birnin da rashin ingantaccen tsari.
Domin neman hanyar rage asarar rayuka a dalilin yawan samun rushewar gine-gine, injiniyoyi da masana harkar gini na ganin tabbas sai gwamnati ta tashi tsaye wajen saka ido ga yadda ake gine-gine da kuma tabbatar da bin ka’idojin da ya kamata.
Domin karin bayani ga rahotan Babangida Jibrin.
Facebook Forum