Wannan zaftare kudaden na zuwa ne yayin da ma’aikatan kananan hukumomin jihar 21 ke ci gaba da hamma ta rashin samun albashi, inda wasu suka shafe fiye da watanni uku babu albashin.
Kamar yadda bayanai ke nunawa an zaftare albashin ne domin gudanar da aikin katin ma’aikata wato ‘ ID card,’ da kungiyar kwadago a jihar ta bukaci a aiwatar inda kungiyar ta bada umarnin da a cire naira N1,500, koda yake ma’aikatan sunce basu san da wannan batu ba.
Wasu ma’aikatan da suka harzuka sun garzaya ofishin akanta janar na jihar domin neman bahasin zaftare musu kudaden da aka yin a fiye da abin da kungiyar kwadagon ta nema.
Don jin hakikanin abin da ya faru wakilin Muryar Amurka ya leka ofishin akanta janar ta jihar Adamawa, to amma ko hakata bata cimma ruwa ba, domin kuwa suna wani taron gaggawa, haka Muryar Amurka ta tuntubi kwamishinan yada labaran jihar Ahmad Sajo, wanda yace zai tuntube wakilin to amma har lokacin hada wannan rahoto babu labari daga gareshi.
To sai dai kuma, a martaninta kungiyar kwadagon jihar NLC, ta bakin shugabanta Kwamared Dauda Maina, tace ba haka suka tsara tun farko ba.
Ya zuwa yanzu shugabanin kungiyar kwadago sunce zasu gana da bangaren gwamnati don gano bakin zaren magance wannan takaddama, kamar yadda shugaban kungiyar kwadagon yayi Karin haske.
Domin karin bayani ga rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Facebook Forum