Ya kara da cewa, suna sadaukar da rayukansu domin kare ‘yan kasarmu daga abokan gaba da suke amfani da kisan wadanda basu ji ba, basu gani ba, wajen yakar rayuwar bil’Adama kanta.
Ya yi wannan furucin ne a jawabinsa wajen tunawa da ‘yan mazan jiya da aka gudanar a makabartar dake Arlington, jim kadan bayan ya ajiye furannin karrama sama da tsofaffin sojoji dubu dari uku da aka binne a makabartar.
Nan ba da dadewa ba ake kyatata zaton shugaba Trump zai sanar da shawarar da ma’aikatar tsaron kasa ta Pentagon ta yanke na kara yawan dakarun Amurka domin ci gaba da yaki a Afghanistan.
Barack Obama bai tsaida shawara a kan bukatar da ma’aikatar tsaron ta gabaar cikin watannin shugabancinsa na karshe ba, a maimakon haka ya barwa shugaban kasar da zai gajeshi, ya kara dakarun da zasu tafi bakin daga a yakin da ya kasance mafi tsawo a tarihin ayyukan sojin kasar.
Yanzu haka akwai sojojin Amurka kimanin dubu takwas da dari hudu a Afghanistan, kwamandoji sun kuma bukaci Karin sojoji dubu biyar.
Facebook Forum